Mambobin APC 5,000 sun sauya sheka zuwa PDP a jihar Ondo

Mambobin APC 5,000 sun sauya sheka zuwa PDP a jihar Ondo

- Akalla mambobin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) 5,000, ne suka sauya sheka zuwa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Ondo

- Olusola Nenuwa, shugaban masu sauya shekar ya bayyana cewa sun yanke shawarar barin APC ne saboda jam’iyya mai mulki ta gazawa mutanen kasar

- Yace gwamnatin Buhari ta gurgunta tattalin arzikin kasar a shekaru uku da rabi da suka gabata, sannan ga yawan rashin aikin yi da kuma yunwa

Rahotanni sun kawo cewa akalla mambobin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) 5,000, ne suka sauya sheka zuwa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a karamar hukumar Akure ta Kudu da ke jihar Ondo.

Olusola Nenuwa, shugaban masu sauya shekar ya bayyana cewa sun yanke shawarar barin APC ne saboda jam’iyya mai mulki ta gazawa mutanen kasar.

Mambobin APC 5,000 sun sauya sheka zuwa PDP a jihar Ondo

Mambobin APC 5,000 sun sauya sheka zuwa PDP a jihar Ondo
Source: Depositphotos

Nenuwa yace gwamnatin shugaba Muhammad Buhari ta gurgunta tattalin arzikin kasar a shekaru uku da rabi da suka gabata, sannan ga yawan rashin aikin yi da kuma yunwa.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Wasu jam’iyyu 10 sun sake hadewa da CUPP domin tsige Buhari

Ya kuma bukaci yan Najeriya da zabi dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar azabe mai zuwa, cewa tsohon mataimakin shugaban kasar na da ikon daukar kasar daga matsalar tattalin arziki.

Nenuna wanda ya kasance mamba a kwamitin kamfen din Rotimi Akeredolu a 2016, yayi alkawarin cewa sabbin mambobin na PDP za su yi kokari don ganin dukkanin yan takarar jam’iyyar a jihar sun yi nasara.

Abiodun Omonijo, shugaban PDP a yankin Akure ta kudu wanda ya karbi bakuncin sabbin mambobin jam’iyyar a madadin shugaban jam’iyyar na jihar ya yaba masu akan hukuncin da suka yanke.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma Legit.ng Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel