Yanzu Yanzu: Wasu jam’iyyu 10 sun sake hadewa da CUPP domin tsige Buhari

Yanzu Yanzu: Wasu jam’iyyu 10 sun sake hadewa da CUPP domin tsige Buhari

- Sabbin jam’iyyun siyasa guda goma sun sake hadewa da jam’iyyar Coalition of United Political Parties (CUPP)

- Hakan na cikin kokarinsu na ganin sun tsige shugaban kasa Muhammadu Buhari da jam’iyyarsa daga mulki a zaben 2019

- CUPP, wacce ke dauke da jam’iyyun siyasa 45, ta gargadi shugaba Buhari ya hakura tn kafin a kayar dashi a zaben

Wasu jam’iyyun siyasa guda goma sun sake hadewa da jam’iyyar Coalition of United Political Parties (CUPP) wadanda ke kokarin ganin sun tsige shugaban kasa Muhammadu Buhari da jam’iyyarsa daga mulki a zaben 2019.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa wasu jam’iyyu siyasa kuma sun mika takardarsu na neman bin sahun masu adawa da gwamnatin APC.

Yanzu Yanzu: Wasu jam’iyyu 10 sun sake hadewa da CUPP domin tsige Buhari

Yanzu Yanzu: Wasu jam’iyyu 10 sun sake hadewa da CUPP domin tsige Buhari
Source: Twitter

Legit.ng ta tattaro cewa CUPP, wacce ke dauke da jam’iyyun siyasa 45, ta gargadi shugaba Buhari ya hakura tn kafin a kayar dashi a zaben.

A lokacin sanya hannu a yarjejeniyar yin aiki tare, CUPP ta hannun wani tsohon gwamnan jihar Osun, Olagunsoye Oyinlola tace abubuwan da ke faruwa a kasar ya nuna karara cewa shugaba Buhari da APC basu shirya tuka jirgin shugabanci a kasar ba.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Bukola Saraki ya amince da sunayen mutum 12 a hukumar majalisar dokoki (kalli jerin sunayen)

Wasu daga cikin sabbin jam’iyyun siyasa da suka hade da CUPP sun hada da Save Nigeria Congress, United Patriots, Reformed and Advancement Party, Alliance for Social Democrats, We the People Nigeria da sauransu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma Legit.ng Hausa

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel