Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya cika shekaru 76 a duniya, kalli wankan da ya sha a yau (Bidiyo)

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya cika shekaru 76 a duniya, kalli wankan da ya sha a yau (Bidiyo)

A yau 17 ga watan Disamba 2018 ya yi daidai da zagayowar ranar haihuwar shugaban kasa Muhammadu Buhari inda ya cika shekaru 76 a duniya.

An haifi shugaba Buhari a rana 17 ga watan Disamba 1942 a garin Daura, jihar Katsina lokacin Najeriya na karkashin mulkin mallaka.

Tuni a dai manyan ‘yan Najeriya suka fara taya shugaban kasar murnar, tare da addua’r Allah ya albarkaci rayuwarsa da kara masa lafiya.

Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, shugaba majalisan dattawa, Bukola Saraki; kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara, da manyan yan siyasa sun aika sakon taya murnarsu ga shugaba Muhammadu Buhari.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma Legit.ng Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel