2019: Kakakin Atiku ya fada ma Buhari cewar kada yayi kamfen da jirgin shugaban kasa

2019: Kakakin Atiku ya fada ma Buhari cewar kada yayi kamfen da jirgin shugaban kasa

- Kakakin dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da kada ya yi asarar kudin masu biyan haraji ta hanyar yin kamfen da jirgin shugaban kasa

- Shuaibu ya gabatar da wannan bukata ne a wani hira da Channels TV

- Ya nusar da cewar Buhari ya yarda cewa tattalin arzikin kasar ya tabarbare a karkashin kulawarsa

Phrank Shuaib, babban mai bayar da shawara na musamman ga dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar, kan harkokin sadarwa ya bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da kada ya yi asarar kudin masu biyan haraji ta hanyar yin kamfen da jirgin shugaban kasa.

Shuaibu ya gabatar da wannan bukata ne a wani hira da Channels TV.

2019: Kakakin Atiku ya fada ma Buhari cewar kada yayi kamfen da jirgin shugaban kasa

2019: Kakakin Atiku ya fada ma Buhari cewar kada yayi kamfen da jirgin shugaban kasa
Source: Facebook

Legit.ng ta tattaro cewa kakakin ya bukaci shugaban kasar da ya yasar da adikon sannan ya daina almuazaranci da kudin masu biyan haraji akan kamfen, inda ya nusar da cewar Buhari ya yarda cewa tattalin arzikin kasar ya tabarbare a karkashin kulawarsa.

A halin da ake ciki, a baya Legit.ng ta rahoto cewa wani malamin addinin Musulunci a Abuja, , Sheikh Abubakar Sadeeq Shaibu, ya gargadi shugaban kasa Muhammadu Buhari da Alhaji Atiku Abubakar das u daina harin junansu a yayinda suke kamfen don neman kujear shugabancin kasar a 2019.

KU KARANTA KUMA: Mun yi nadamar zaben Buhari - Kungiyar matasan arewa

Malamin ya bayyana hakan ne a wajen bikin Maulidi a Abuja a ranar Asabar, 15 ga watan Disamba. Yace hakan abun kunya ne ganin yan takarar guda biyu na kaiwa junansu farmaki yayinda suke kamfen.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma Legit.ng Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel