Bukola Saraki: Sanatan PDP ya maidawa Bola Tinubu raddi

Bukola Saraki: Sanatan PDP ya maidawa Bola Tinubu raddi

Mun ji cewa wani Sanata da ke wakiltar Jihar Kwara a Majalisar Dattawa, Rafiu Ibrahim ya maidawa babban Jigon APC, Bola Tinubu, martani na sukar shugabancin Majalisar Tarayya da yayi kwanakin baya.

Bukola Saraki: Sanatan PDP ya maidawa Bola Tinubu raddi

Sanatan Jihar Kwara ya caccaki Jigon APC Tinubu
Source: Depositphotos

Sanata Rafiu Ibrahim mai wakiltar Kwara ta Kudu a Majalisar Tarayya yayi tir da kalaman Bola Tinubu na cewa wasu mutanen kawai ne su ka hana a zabi Sanata Ahmad Lawan a Majalisar Dattawa bayan an kafa Gwamnatin APC.

Ibrahim yace bai kamata irin su Bola Tinubu su rika sakin baki su na magana a matsayin su na Dattawa ba. Ibrahim yayi Allah-wadai da sunayen banzan da Tinubu ya rika kiran wadanda su ka marawa Sanata Bukola Saraki baya a 2015.

KU KARANTA: Wani ‘Dan APC ya maka Uwar-Jam’iyya a gaban Kotu

Sanatan yace a matsayin Bola Tinubu na Dattijo, bai dace ya soki wadanda ba su goyon bayan Bukola Saraki ba domin kuwa ba a san Dattawa da haka ba. ‘Dan Majalisar yace bai dace Tinubu ya tado abin da ya faru a baya ba.

‘Dan Majalisar na Kudancin Kwara yake cewa su Bola Tinubu ne su ka fitini Bukola Saraki da shari’a a gaban Kotu. Sanatan yace a karshe bayan an gaza yin sulhu a APC ne su ka fice da wasu ‘Yan Majalisa su ka koma PDP.

Rafiu Ibrahim ya nuna cewa tsohon Gwamnan na Legas, Asiwaju Bola Tinubu ne su ka haddasa rigimar da ta barke a APC har ta kai wasu ‘Yan Majalisan Kasar su ka tattara su ka koma Jam’iyar hamayya ta PDP.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel