Aisha Buhari ta yi hasashen komawar Emmanuel APC

Aisha Buhari ta yi hasashen komawar Emmanuel APC

- Uwargida shugaban kasa Aisha Buhari tayi hasashen cewa gwamnan jihar Akwa Ibom, Udom Emmanuel da uwargidansa, Martha za su koma jam’iyyar APC

- Aisha ta bayyana hakan a Uyo yayin kaddamar da shirin bayar da tallafi ga matan Akwa wanda gidauniyar Future Assured ta dauki nauyi

- A cewarta abunda ya faru a filin jirgin sama na Victor Attah lokacin da ta isa jihar alamu ne na cewa jihar Akwa Ibom za ta zamo jihar APC

Uwargida shugaban kasa, Hajiya Aisha Buhari tayi hasashen cewa gwamnan jihar Akwa Ibom, Udom Emmanuel da uwargidansa, Martha za su koma jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Ta yi Magana a Uyo yayin kaddamar da shirin bayar da tallafi ga matan Akwa wanda gidauniyar Future Assured ta dauki nauyi.

Aisha Buhari ta yi hasashen komawar Emmanuel APC

Aisha Buhari ta yi hasashen komawar Emmanuel APC
Source: Depositphotos

Aisha tace abunda ya faru a filin jirgin sama na Victor Attah lokacin da ta isa jihar alamu ne na cewa jihar Akwa Ibom za ta zamo jihar APC.

Ta ce: “A gare ni abunda ya faru a filin jirgin siyasa ce kawai, amma idan aka zo ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, wani yunkuri ne, kuma muna da Sanata Akpabio a Akwa Ibom domin ya jagoranci yunkurin.

KU KARANTA KUMA: 2019: Babu madadin shugaba Buhari - Minista

“Kamar yadda kuka sani, shugaban kasar mutum ne mai muhimmanci, sannan kuma duk wanda ya yartda da manufarsa, sai suyi siyasa da mutunci. Abunda ya faru a fiin jirgi ya nuna cewa kusan kowa ya shiga APC a Akwa Ibom, sannan kuma ba da jimawa ba Mista Udom Emmanuel da uwargidansa za su bi sahun mu.”

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma Legit.ng Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel