2019: APC ta mayar da martani kan zarginta da shirya magudin zabe da PDP ta yi

2019: APC ta mayar da martani kan zarginta da shirya magudin zabe da PDP ta yi

- Jam'iyyar APC ta mayar da martani a kan zargin cewa tana shirin tafka magudi a zaben 2019 da PDP ta yi

- APC ta ce tsoron shan kaye ne ya sanya PDP ta fara yada karerayi da farfaganda a maimakon ta mayar da hankali kan nata yakin neman zaben

- APC ta ce shugaba Muhammadu Buhari ya fara kamfen dinsa tun shekaru uku da suka gabata ta hanyar cika alkawurran da ya dauka wa 'yan Najeriya

A jiya, Lahadi ne Jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) tayi zargin cewa ana shirya yadda za a gudanar da magudin zabe a babban zaben 2019.

Dalilin ta kuwa shine duk da cewa saura kwanaki 61 kafin zabe, har yanzu shugugaba Muhammadu Buhari da jam'iyyar APC ba su fitar da tsarin yakin neman zaben ba saboda suna shirin yin magudi.

2019: APC ta mayar da martani kan zarginta da shirya magudin zabe da PDP ta yi

2019: APC ta mayar da martani kan zarginta da shirya magudin zabe da PDP ta yi
Source: Twitter

Sai dai tuni APC ta musanta zargin, ta ce a maimakon jam'iyyar ta PDP ta mayar da hankali a kan muhimman abubuwa da ke gabanta, ta sanya idanu a kan harkokin jam'iyyar APC.

DUBA WANNAN: A karon farko tun bayan faduwar PDP, Adamu Mu'azu ya shigo Najeriya

Sanarwar da ta fito daga bakin mai magana da yawun jam'iyyar PDP, Kola Ologbondiyan ta ce shugaba Muhammadu Buhari a kidime ya ke.

Wani bangare na sanarwar ta ce: "A ko ina a duniya, shugbanni masu kishin kasa da ke neman zarcewa suna fadawa al'umma ayyukan da su kayi da abinda za su sake yi amma shugaban kasar mu da APC suna da yiwa abokan hamayya barazana, kawo baraka a INEC da kirkirar rumfunan zabe na bogi da kin amincewa da kasafin kudi da kin saka hannu a kan dokar zabe da zai doshe kafafen tafka magudin zabe."

PDP ta kuma yi ikirarin cewa shuagaba Buhari ya gaza samar da tsaro a kasa, ya gaza samar da ayyukan ya raba kan 'yan kasa kana ya gurgurtara da tattalin arzikin Najeriya.

A bangarensa, Sakataren watsa labarai na jam'iyyar APC, Mallam Lanre Issa-Onilu ya ce abin mamaki ne yadda PDP tayi watsi da yakin neman zabenta ta fara sanya idanu a kan yakin neman zaben APC, ya ce shugaba Buhari ya fara kamfen dinsa tun shekaru uku da suka gabata ta hanyar ayyukan raya kasa da ya keyi.

Kazalika, Ciyaman din BMO, Niyi Akinsaju ya ce zargin na PDP abin dariya ne inda ya kara da cewa suna tsoron shan kaye ne kawai. Ya yi kira da jam'iyyar ta PDP ta mayar da hankali a kan yakin neman zaben ta a maimakon yadda jita-jita da babu hujja.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel