Manyan shugabannin Musulunci 3 sun tsallake rijiya da baya a hannun masu garkuwa da mutanea Rivers

Manyan shugabannin Musulunci 3 sun tsallake rijiya da baya a hannun masu garkuwa da mutanea Rivers

Rahotanni sun kawo cewa wasu shugabannin kungiyar Tijaniya reshen jihar Rivers guda uku sun yi nasarar kubuta daga hannun wadanda suka yi garkuwa da su.

Uku daga cikin shugabannin musulunci hudu da masu garkuwa da mutane suka sace a jihar Rivers sun tsere daga hannun yan ta’addan a dajin Ibaa da ke karamar hukumar Emoha a daren ranar Lahadi, 1 ga watan Disamba.

Tsoro ya cika zukatan iyalan Alhaji Bello Usman, wanda ke cikin shekarunsa na 50s wanda yan ta’addan ska yasar a dajin tun daren ranar Alhamis bayan ya yanke jiki ya fadi sau uku yayinda mas garkuwan ke jan shi zuwa mafakarsu a dajin Ibaa.

Daga cikin wadanda suka tsere daga hannn yan ta’addan sun hada da Alhaji Mukadam Aliyu Abdulhamid, babban sakataren kungiyar Tijaniyah na jihar Rivers.

Manyan shugabannin Musulunci 3 sun tsallake rijiya da baya a hannun masu garkuwa da mutanea Rivers

Manyan shugabannin Musulunci 3 sun tsallake rijiya da baya a hannun masu garkuwa da mutanea Rivers
Source: Depositphotos

Wata majiya ta kusa da kungiyar Tijaniyan a Rivers ta bayyana cewa masu garkuwan sun tafi dasu zuwa mafakarsu a dajin Ibaa bayan sun rufe masu idadunsu.

Cikin tsakar dare, wadanda aka sacen suka daina jin hayaniyar wadanda suka yi garkuwa da su. Sauran wadanda aka sace uku sai suka fara ihun a basu ruwa su sha don janyo hankali masu garkuwan amma sai suka ji shiru.

Don haka suka tabbata cewa masu garkuwan sun bar su, na dan lokacin nan, sai daya daga cikinsu yayi kacaniyar cire igiyar da aka daure su das hi. Cikin sa’a sai yayi nasara sannan ya kwance sauran suka kuma bude idanunsu.

Sai ga sojoji suka kais u Port Harcourt, amma sai suka sauke su a shataletalen Rumuokoro da misalin karfe 4pm sannan suka basu kudin mota N2,000 zuwa gidajensu.

KU KARANTA KUMA: 2019: Babu madadin shugaba Buhari - Minista

Da yake tabbatar da tserewan shugabannin uku, Khalifah Murtala Sulaiman Abdulsalam, wanda ya kasance shugaban kungiya na jihar Rivers, ya bayyana yadda suka tsere da kuma yadda wasu mambobin coci suka kula da su.

Ya bayyana cewa Alhaji Mukadam Aliyu Abdulhamid wanda ya kasance babban sakataren kungiyar na cikin wadanda suka tsere. Sauran sune Alhaji Ibrahim Baba da kuma Alhaji Bashir, wani makaniki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma Legit.ng Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel