Shugaba Buhari zai doke Atiku Abubakar a zaben 2019 – Inji Ganiyu Johnson

Shugaba Buhari zai doke Atiku Abubakar a zaben 2019 – Inji Ganiyu Johnson

- Wani Jigon APC ta bayyana cewa Atiku zai sha kashi a zaben 2019

- Johnson yace ko Buhari bai yi mukabala da Atiku ba zai kai labari

- Babban ‘Dan APC yace ba muhawara ke sa a ci zabe a Najeriya ba

Mun samu labari cewa daya daga cikin manyan APC a cikin Kudancin Najeriya, Ganiyu Johnson ya bayyana cewa Shugaban Kasa Buhari zai yi wa Atiku fintinkau a zaben 2019. Johnson yace APC ce za ta lashe zaben da za ayi a badi.

Tsohon kwamishinan ayyuka na Jihar Legas, Ganiyu Johnson ya bayyanawa ‘Yan Jarida cewa babu yadda Atiku Abubakar zai yi da Buhari a 2019. Johnson yace ko da Buhari bai tsaya muhawar da PDP ba, zai yi nasara hankali kwance.

KU KARANTA: Atiku Abubakar yana cigaba da shiryawa zaben 2019 gadan-gadan

Tsohon kwamishinan yace a Najeriya jama’a ba su damu da muhawarar zabe ba. Johnson ya kuma ce adadin Kananan Hukumomin da ake da su a Jihar Kano da Jigawa kurum sun zarce yawan duka Kananan Hukumomin Inyamurai.

Babban ‘Dan siyasan na Legas wanda yanzu yake neman kujerar Majalisa yace ba za a iya gane wanda zai yi nasara a zabe wajen mukabala ba, a cewar sa akwai ‘Yan kauye da Mutanen da ke kasuwa da babu ruwan su da wani dogon surutu.

Ganiyu Johnson wanda aka fi sani da GAJ dai yace babban abin da ke cin zabe shi ne yi wa al’umma aiki. Kwanaki ne Johnson yayi murabus daga mukamin sa domin ya nemi kujerar Majalisar Tarayya na Yankin Oshodi Isola II na Legas.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel