Matashi ya fadawa Kotu a tsige Onilu a nada sa Sakataren yada labarai na APC

Matashi ya fadawa Kotu a tsige Onilu a nada sa Sakataren yada labarai na APC

Wani fitaccen Marubuci kuma Mawallafi a shafukan yanar gizo, Abubakar Usman ya shiga Kotu da Jam’iyyar APC mai mulki inda ya ke karar wani mataki da Jam’iyyar ta dauka wajen bada mukami.

Matashi ya fadawa Kotu a tsige Onilu a nada sa Sakataren yada labarai na APC

Bolaji Abdullahi ya bar APC yana PDP tare da Bukola Saraki.
Source: UGC

Kamar yadda Jaridar Premium Times ta rahoto, Mista Abubakar Usman ya kai karar Jam’iyyar APC a gaban Kotu ne a dalilin nada Lanre Issa-Onilu da aka yi a matsayin sabon Sakataren yada labarai na Jam’iyyar mai mulki.

Usman ya fadawa Kotu cewa shi ya fi dacewa da kujerar Sakataren yada labarai na Kasa a Jam’iyyar APC bayan murabus din da Bolaji Abdullahi yayi a Watan Agustan da ya wuce. Usman ya nemi a tsige Malam Lanre Issa-Onilu.

KU KARANTA: Wata Kungiya ta matsa lamba a binciki wani Gwamnan APC

Malam Usman shi ne ya zo na biyu a zaben da aka yi na mukamin Sakataren yada labarai na APC, inda Lanre Issa-Onilu ya zo na uku yayin da Duro Meseko ya kare a na hudu a zabukan da APC ta shirya a karshen Watan Yuni.

Sai dai kuma Uwar Jam’iyyar tayi watsi da wannan tsari, ta nada Issa-Onilu ya gaje Bolaji Abdullahi. Wannan Matashin yace APC tayi watsi da kundin tsarin mulkin kasa da dokokin zabe da kuma kuma ka’idar zaben APC.

Usman wanda aka fi sani da Abu Sidiqu ya nemi APC da kuma INEC su bi doka su nada sa kan wannan kujera a sakamakon ajiye mukamin da Abdullahi wanda yayi nasara a zaben na APC yayi. Yanzu haka Abdullahi ya koma PDP.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a hausah

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel