2019: Shugaba Buhari bai shirya ma zabe ba - PDP

2019: Shugaba Buhari bai shirya ma zabe ba - PDP

- Jam’iyyar PDP ta bayyana cewa tunda har Shugaban Buhari ya gaza kafa kungiyar kamfen dinsa kwanaki 61 zuwa zaben shugaban kasa toh lallai alamu ne na cewa bai shirya ma zaben ba

- PDP ta zargi APC da kin kafa manufar kamfen saboda suna kulla maikircinsu da hukumar zabe mai zaman kanta domin yin magudin zabe

- Sakataren jam’iyyar, Kola Ologbodiyan yace Buhari ya shiga zullumi akan mafi akasarin yan Najeriya da suka dawo daga rakiyan shi da gwamnatinsa wacce ta gaza

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta bayyana cewa tunda har Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya gaza kafa kungiyar kamfen dinsa, kwanaki 61 zuwa zaben shugaban kasa na watan Fabrairu, toh lallai alamu ne na cewa bai shirya ma zaben ba.

Jam’iyyar ta kara da cewa shugaban kasar da jam’iyyarsa ta All Progressives Congress (APC) sun gaza kafa manufar kamfen saboda suna kulla maikrcinsu da hukumar zabe mai zaman kanta (INEC), a karkashin Farfesa Mahmood Yakubu, don yin magudin zabe.

2019: Shugaba Buhari bai shirya ma zabe ba - PDP

2019: Shugaba Buhari bai shirya ma zabe ba - PDP
Source: Depositphotos

A cewar wata sanarwa daga babban sakataren labarai na PDP, Kola Ologbodiyan, yace a bayyane yake cewa shugaba Buhari ya shiga zullumi akan mafi akasarin yan Najeriya da suka dawo daga rakiyan shi da gwamnatinsa wacce ta gaza.

Yace shiyasa shugaban kasar ya gaza kafa kwamitin kamfen dinsa tun bayan da ya kaddamar da manufofin zabensa na mataki na gana wato ‘Next Level’.

KU KARANTA KUMA: Yau ne zagayowar ranar haihuwar Shugaban kasa Buhari

A wani lamari na daban, mun ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa abinda ya dace shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi shine yayi murabus kan kalaman da yayi game da tattalin arzikin Najeriya.

Atiku ya ce gazawar Buhari da rashin kwarewar sa wajen jan ragamar mulkin kasa da saita tattalin arziki ya fito karara inda ya furta da bakin sa cewa a karkashin sa tattalin arzikin kasar nan ya durkushe.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma Legit.ng Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel