Kungiyoyi 3 sun nemi Buratai ya yi bayani kan yadda ya kashe kudaden yaki da Boko Haram

Kungiyoyi 3 sun nemi Buratai ya yi bayani kan yadda ya kashe kudaden yaki da Boko Haram

Wasu kungiyoyin jama’a sun rubuta wa shugaban hafsan sojojin Najeriya, Tukur Buratai wasika, inda suka bukaci ya yi bayani dalla-dalla a rubuce, kan yadda ya kashe kudaden da aka ware masa domin yaki da ta’addanci daga 2015 har zuwa 2017.

Kungiyoyin da suka hada da SERAP, sun nemi Laftanar Janar Buratai ya yi bayanin adadin kudaden da ya kashe daga 2015, 2016 da 2017 a kan Operation Lafiya Dole, Operation Safe Haven, Operation Pethon Dance, Operation Ruwan Wuta, Operation Mesa, Operation Harbin Kunama, Operation Tsare Teku da Operation Harbin Kunama.

Wasikar ya samu sa hannun shugaban kungiyar SRAP, , Bamisope Adeyanju, Seun Akinyemi da kuma Atiku Samuel na BudgIT.

Kungiyoyi 3 sun nemi Buratai ya yi bayani kan yadda ya kashe kudaden yaki da Boko Haram

Kungiyoyi 3 sun nemi Buratai ya yi bayani kan yadda ya kashe kudaden yaki da Boko Haram
Source: UGC

A cewarsu akwai bukatar ayi wa al’umma bayanai dalla-dalla domin warware masu abunda ya shige masu duhu domin su daina neman sanin yadda ake tafiyar da kudaden.

Sun ci gaba da cewa idan har aka yi kwanaki 14 ba su ji bayanin komai daga Buratai ba, to za su maka shi kotu saboda a tilasta shi fitowa da bayanan.

KU KARANTA KUMA: Ya kamata Buhari yayi murabus kan cewa da yayi wai tattalin arzikin kasa ya tabarbare – Atiku

Sun kuma ci gaba da cewa an kashe makudan kudaden wajen yaki da Bokon Haram, a tsakanin shekarun 2015, 2016 da 2017 masamman a yankin Arewa maso Gabas, amma babu wata alamar da ke nuna cewa kudaden da aka kashe sun kara wa sojojinmu kuzari da kumajin yaki sosai.

Bayan wannan sun kuma yi korafin cewa kudaden da aka kashe a yaki da Boko Haram ba su nuna alamar samun wani gagarimin ci gabaci gaba a yadda ake yaki da yan ta’addan ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma Legit.ng Hausa

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel