Kungiyar HEDA ta nemi a binciki zargin da ke kan Gwamna Ganduje

Kungiyar HEDA ta nemi a binciki zargin da ke kan Gwamna Ganduje

Mun ji labari cewa wata Kungiya mai zaman kan-ta a Jihar Kano tayi kira da babban Alkalin Najeriya ya soma gudanar da bincike a kan zargin da ke wuyan Gwaman Jihar Kano Abdullahi Ganduje na karbar rashawa.

Kungiyar HEDA ta nemi a binciki zargin da ke kan Gwamna Ganduje

Ana zargin Gwamna Abdullahi Ganduje da karbar rashawa.
Source: Facebook

Kungiyar HEDA ta nemi Alkalin Alkalai na Najeriya, Mai shari’a Walter Onnoghen, yayi amfani da sashe na 52 na dokar Hukumar ICPC mai yaki da barayin Kasar nan domin ta fara gudanar da bincike kan Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.

Ana zargin Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano ne da karbar rashawa bayan wata Jarida ta fito da bidiyoyin da ke nuna Gwamnan yana karbar Dalolin kudi daga hannun wadanda ake tunani ‘Yan kwangila ne a Jihar Kano.

Shugaban wannan Kungiya ta HEDA watau Olanrewaju Suraju, ya aikawa Hukomomin Najeriya wasika a takarda inda ya nemi su yi maza-maza su fara binciken Gwamnan kamar yadda wani sashe na dokar ICPC ya bada dama a dokar kasa.

KU KARANTA: Gwamnatin jihar Ekiti ta kulle wasu manyan gine-ginen Fayose

Kamar yadda mu ka samu labari daga Jaridar Premium Times, Kungiyar HEDA mai zaman kan ta nemi a soma bincike ta na kuma mai yin tir da yadda Gwamnan yayi watsi da zaman da aka yi a Majalisa, inda ya aika wani kwamishinan sa.

Gwamna Ganduje dai ya musanya gaskiyar bidiyoyin da Jaridar Daily Nigerian ta saki inda yace siddabaru ne kurum na fasahar zamani. Haka kuma Kotu ta haramtawa ‘Yan Majalisar dokokin Jihar gabatar da wani bincike a kan lamarin.

Dazu kun ji cewa an soma yakin neman zaben Gwamna Abdullahi Ganduje na APC da kashe-kashe a Jihar Kano wasu su ka bakunci lahira a wajen kamfen din Jam’iyyar ta APC da aka shirya a karshen mako.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel