Buhari zai mika mulki ga dan kabilar Igbo a 2023 - Sakataren gwamnatin tarayya

Buhari zai mika mulki ga dan kabilar Igbo a 2023 - Sakataren gwamnatin tarayya

Jam'iyyar APC ta kara jaddada aniyarta kan cewar shugaba Buhari zai mika mulki ga dan kabilar Igbo bayan gama wa'adinsa a shekarar 2023, a cewar sakataren gwamnatin tarayya, Boss Gida Mustapha.

Sai dai wannan mataki na Mustapha ya saba da na ministan aiyuka, gidajen, da lantarki, Babatunde Raji Fashola, na cewar shugaba Buhari zai mika mulki ga dan kabilar Yoruba a 2023.

Da yake magana yayin jawabi ga kwamitin masu goyon bayan Buhari a Umuahia, jihar Abiya, a karshen makon na, Mustapha ya bayar da tabbacin cewar shugaba Buhari ga dan kabilar Igbo idan ya kammala wa'adinsa.

A cewar sa, hanya mafi sauki da 'yan kabilar zasu samu damar yin mulkin Najeriya shine su goyawa Buhari a zabukan shekarar 2019.

Buhari zai mika mulki ga dan kabilar Igbo a 2023 - Sakataren gwamnatin tarayya

Sakataren gwamnatin tarayya; Boss Gida Mustapha
Source: Depositphotos

Mustapha, da yake magana ta bakin wakilinsa, Mista Gideon Sammani, ya ce ya yi farinciki da karbuwar da jam'iyyar APC ke kara samu a yankin kudu maso gabas na 'yan kabilar Igbo. Ya kara da cewar daga abinda ya gani yana da yakinin cewar shugaba Buhari zai lashe zabe a yankin.

DUBA WANNAN: An kashe mutane 4 a wurin kaddamar da kamfen din Ganduje a Kano

Ya ce shugaba Buhari ya nuna kauna da soyayya ga yankin kudu maso gabas da 'yan kabilar Igbo ta hanyar mayar da hankali ga gina babbar gadar Neja ta biyu.

A jawabinsa, Injiniya Chemberline Adiaso, shugaban kwamitin masu goyon Buhari a yankin, ya ce shugaba Buhari ya tabbatar da cewar shi mutum ne mai kima da daraja.

Ya kara da cewar zasu goyi bayan shugaba Buhari don samun cikar burinsu na samun mulkin Najeriya a 2023.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel