Wani bidiyon sojojin Najeriya 2 da suka kashe wasu kauyawa ya jawo cece-kuce

Wani bidiyon sojojin Najeriya 2 da suka kashe wasu kauyawa ya jawo cece-kuce

Wani faifan bidiyo da mu gama tantance sahihancin sa ba da kuma yake yaduwa a yanar gizo musamman ma dandalin sada zumunta tamkar wutar dauke da fuskokin wasu mutane sanye da kayan sojoji da kuma suka kashe wasu kauyawa na cigaba da jawo cece-kuce.

Faifan bidiyon dai kamar yadda muka samu, wani ma'abocin anfani da dandalin zumunta na Facebook ne mai suna Auwal Mustapha ya fara wallafa shi kafin daga bisani jama'a suyi ta yada shi suna kuma fadin albarkacin bakin su game da shi.

Wani bidiyon sojojin Najeriya 2 da suka kashe wasu kauyawa ya jawo cece-kuce

Wani bidiyon sojojin Najeriya 2 da suka kashe wasu kauyawa ya jawo cece-kuce
Source: Facebook

KU KARANTA: EFCC ta kama wani gidan tsohon gwamna na Naira miliyan 500

Ma'aikacin Legit.ng Hausa wadda ya samu ganin bidiyon ta ruwaito cewa yana dauke ne da mutane biyu sanye da kayan sojoji sai kuma wasu kauyawa suma su biyu tare da jakin su kafin daga bisani kuma a nuna su a mace.

Sai dai yayin da wasu ke tofin Allah-tsine game da bidiyon inda suke bayyana rashin dacewar hakan wasu kuma na ganin cewa wata kila 'yan ta'adda ne ko kuma barayin shanu ko mutane da suka addabi al'umma musamman ma ganin cewa ba'a bayyana inda hakan ta faru ba.

Da yake yin tsokaci game da bidiyon, kakakin rundunar sojin Najeriya Kanal Usman Kukasheka ya bayar da tabbacin cewa rundunar zata yi bincike akan lamarin kuma zata hukunta dukkan wanda aka samu da laifin yin kisa ba tare da hakki ba.

Ga dai bidiyon nan:

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel