Yadda karuwai da 'yan fashi suka hana Sanata Lawan zama shugaban majalisar dattijai - Tinubu

Yadda karuwai da 'yan fashi suka hana Sanata Lawan zama shugaban majalisar dattijai - Tinubu

Jagoran jam'iyyar APC na kasa, Bola Tinubu, ya yi wani shagube ga wadanda suka hana Sanata Ahmed Lawan zama shugaban majalisar dattijai duk da kasancewar shine wanda shugabannin APC da jiga-jigan jam'iyyar ke goyon baya.

Tinubu ya bayyana cewar karuwai da 'yan fashi irin na siyasa ne suka hana Lawan zama shugaban majalisar dattijai.

Tinubu ya yi wannan kalami ne a jiya, Asabar, yayin da yake gabatar da jawabi a wurin taron murnar cikar gwamna Abiola Ajimobi shekaru 69 wanda aka yi a jihar Oyo.

Tinubu ya kara da cewar wadannan karuwai da 'yan fashi sun hana Lawan zama shugaban majalisar dattijan ne saboda son biyan wasu bukatunsu.

Yadda karuwai da 'yan fashi suka hana Sanata Lawan zama shugaban majalisar dattijai - Tinubu

Tinubu
Source: Depositphotos

Tsohon gwamnan ya kara da cewar ya ga nagartar shugabanci a tare da Sanatan, hakan ya saka shi yanke shawarar goya masa baya domin ya zama shugaban majalisar dattijai aka haramta masa duk akidun shi na son ganin an kawo cigaba mai ma'ana.

DUBA WANNAN: Yunkurin maye Buhari da Osinbajo: Ango Abdullahi ya yi karin haske

A cewar Tinubu, "Ina godiya gareka Sanata Lawan. Kai misali ne na irin hazikan 'yan siyasa dake kishin kasa, irinku basu da yawa.

"Akwai nagarta irinta shugabanci a tare da kai. Mun san kai ne ka cancanta amma karuwai da 'yan fashi irin na siyasa da 'yan koronsu suka haramta maka don biyan bukatar kansu."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel