Kasafin 2019: Ma'aikatan majalisa zasu fara yajin aikin gargadi

Kasafin 2019: Ma'aikatan majalisa zasu fara yajin aikin gargadi

- PASAN, kungiyar ma'aikatan majalisar Najeriya ta bayar da sanarwar fara yajin aikin gargadi na kwankaki hudu daga gobe, Litinin

- Bature Mohammed, shugaban kungiyar, ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya, Asabar, jim kadan bayan fitowar shugabannin kungiyar daga wani taron gaggawa

- Ko a ranar 4 ga wata sai da ma'aikatan majalisar suka gudanar da zanga-zangar da ta kai ga hana zaman mambobin majalisar tarayya zama

Kungiyar ma'aikatan majalisar Najeriya (PASAN) ta bayar da sanarwar fara yajin aikin gargadi na kwankaki hudu daga gobe, Litinin.

Shugaban kungiyar, Bature Mohammed, ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya, Asabar, jim kadan bayan shugabannin kungiyar sun gudanar da wani taron gaggawa.

Duk da shugaba Buhari zai gabatar da kasafin kudin shekarar 2019 a ranar Laraba, 19 ga wata, Mohammed ya ce yajin aikin zai kai har ranar Alhamis, 20 ga wata.

Kasafin 2019: Ma'aikatan majalisa zasu fara yajin aikin gargadi

Ma'aikatan majalisa zasu fara yajin aikin gargadi
Source: Depositphotos

Mohammed ya kara da cewa zasu shiga yajin aikin ne domin neman hakkokinsu da suka makale a hannun shugabannin majalisar.

DUBA WANNAN: Yanzu ne lokacin da zamu kawo karshen ta'addancin kungiyar Boko Haram - Buhari

Shugaban ya shawarci dukkan mambobin kungiyar PASAN da su kauracewa wurin aikinsu.

Ko a ranar 4 ga wata sai da ma'aikatan majalisar suka gudanar da zanga-zangar da ta kai ga hana zaman mambobin majalisar tarayya zama.

Daga cikin bukatun da ma'aikatan majalisar ke nema akwai batun inganta yanayin aikinsu, karin girma da biyan karin kashi 28 a albashinsu kamar yadda yake cikin kunshin kasafin 2018.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel