Yadda sojojin Nigeria suka nemi mafaka a sabon harin da Boko Haram ta kai Borno

Yadda sojojin Nigeria suka nemi mafaka a sabon harin da Boko Haram ta kai Borno

- Mayakan Boko Haram sun kai wani sabon hari a jihar Borno, wanda ya tilasta wasu dakarun soji tarwatsewa tare da neman mafaka a makwaftan garuruwa

- Wannan harin dai shine na uku da aka kaiwa kauyen cikin watanni uku

- Sai dai duk wani yunkuri na jin ta bakin Sani Usman, mai magana da yawun rundunar sojin kasar kan wannan sabon harin ya ci tura

Rahotannin da Legit.ng Hausa ke samu na nuni da cewa wasu dakarun soji sun tarwatse don neman mafaka a lokacin da 'yan ta'addan Islamic State in West Africa (ISWA), wani tsagi na kungiyar Boko Haram suka kai sabon hari a Gudumbali, karamar hukumar Guzamala da ke jihar Borno a ranar Juma'a.

An ruwaito gidan talabijin na Channels TV ta dauki rahoton wani mazaunin yankin da harin ya shafa na cewa 'yan ta'addan sun yi awon gaba da kayayyakin abinci tare da warewa da wasu bindigogi mallakin dakarun sojin kasar.

Wannan harin dai shine na uku da aka kaiwa kauyen cikin watanni uku.

KARANTA WANNAN: Zaben 2019: PDP na son jefa rayukan ma'aikatanmu cikin hatsari - INEC

Yadda sojojin Nigeria suka nemi mafaka a sabon harin da Boko Haram ta kai Borno

Yadda sojojin Nigeria suka nemi mafaka a sabon harin da Boko Haram ta kai Borno
Source: Twitter

Jaridar TheCable ta tattara rahoto kan cewar har zuwa yanzu wasu sojoji da harin ya shafa na ci gaba da samun mafaka a wani sansanin soji da ke Damasak, wani kauye da ke kusa da Gudumbali.

"Dakarunmu sun tarwatse a Gudumbali, har wasu sun shiga Kukawa," wani jami'in soji a rundunar ya shaidawa TheCable a safiyar ranar Lahadi.

A yayin da rundunar sojin kasar ke cewa tuni ta karya lagon mayakan Boko Haram tare da kawo karshensu, shi kuwa Abubakar Elkanemi, Shehun Borno, ya fito ya bayyana cewa har yanzu al'ummar iihar na ci gaba da fuskantar hare hare.

Sai dai duk wani yunkuri na jin ta bakin Sani Usman, mai magana da yawun rundunar sojin kasar kan wannan sabon harin ya ci tura.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel