Wata sabuwa: Dan takarar gwamna a jihar Ogun na APC zai rasa tuta

Wata sabuwa: Dan takarar gwamna a jihar Ogun na APC zai rasa tuta

- Ana zargin Dapo Abiodun bayyi bautar kasa ba

- Dama karfa karfa ce aka yi aka dora shi

- Jihohin Imo, Ogun da Zamfara suna girgidi bayan da gwamnoni bassu son wadanda aka turo

Wata sabuwa: Dan takarar gwamna a jihar Ogun na APC zai rasa tuta

Wata sabuwa: Dan takarar gwamna a jihar Ogun na APC zai rasa tuta
Source: Facebook

Har yanzu dai tana kasa tana dabo a jihohin da APC tayi wa qaqaben 'yan takara, bayan ga wadanda gwamnoni keso.

APC da mulkinta a jihohin Imo, Ogun da Zamfara suna girgidi bayan da gwamnoni bassu son wadanda aka turo daga Abuja, lamari da ta kai ma wasunsu ke cewa sai dai kar jam'iyyar taci zabe a jihar don su basu yi.

An ma jiyo wasunsu suna cewa duk wanda Oshiomhole ya turo sulhu, kashe shi zasu yi, ko kuma a tada yaki a jihar tasu, ko a mutu ko ayi rai.

DUBA WANNAN: A gaskiya PDP na sanya ma'aikatanmu cikin hadari - INEC ta koka

Dapo Abiodun dai, shine dan takara da uwar jam'iyya ta baiwa tuta. Sai dai kuma an gano wai ashe bayyi bautar kasa ba, ko kuma bayyi kaatu ba.

A yadda aka gano dai, ya yi jami'a, wanda in hakan ne, lallai sai ya kawo takardar bautar kasa, amma tunda bayyi bautar kasar ba, kawai sai ya rubuta ai ko jami'ar bayyi ba, wai iyakarsa Sakandare, ssai ya shiga kasuwanci.

In iyaka sakandare mutum yayi, a doka ba sai yayi bautar kasa ba, kuma zai iya tsayawa takara da takardar koda iya ita garai.

Majiyarmu dai na bi mana kadin yadda lamarin zai qarke, ko gwamnan jihar ta Obasanjo, Amosun da dama yana son ya tsayar da wani ne zai ci ribar hakan.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa.

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel