Yunkurin maye Buhari da Osinbajo: Ango Abdullahi ya yi karin haske

Yunkurin maye Buhari da Osinbajo: Ango Abdullahi ya yi karin haske

Shugaban kungiyar dattijan arewa (NEF), Farfesa Ango Abdullahi, ya musanta cewar da hannunsa a yunkurin kawar da shugaba Buhari domin maye gurbinsa da mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo.

Wasu rahotanni dake fitowa kwanan nan sun bayyana yadda manyan arewa suka fara kulla tuggun yadda za nada Osinbajo a matsayin shugaban kasa lokacin da shugaba Buhari ke zaman jinya a kasar Ingila.

An bayyana gungun manyan arewa dake zaune a Kaduna da jagorantar kulle-kullen ganin Osinbajo ya maye gurbin Buhari tare da nada Farfesa Ango a matsayin sabon mataimakin shugaban kasa.

Sai dai a wata ganawa da yayi da jaridar Vanguard, Farfesa Ango ya bayyana cewar babu wasu gungun manyan arewa mazauna Kaduna da jama'a ke magana a kansu.

Yunkurin maye Buhari da Osinbajo: Ango Abdullahi ya yi karin haske

Farfesa Ango Abdullahi
Source: Depositphotos

"Batun wasu manya dake zaune a Kaduna tunanin jama'a ne kawai. Yadda kowa ya ji labarin haka nima na ji shi.

"Maganar cewa ina daga cikin manyan arewa da suka tattauna maye gurbin Buhari da Osinbajo ba gaskiya bane, ban ma san zancen ba.

"Hatta jita-jitar da ake yadawa cewar dattijan arewa sun gana tare da amincewa a kan batun maye gurbin Buhari ba gaskiya bane balle a yi zancen wani ya amince ko bai amince ba.

DUBA WANNAN: 2019: Shugabannin jam'iyyar SDP 37 sun yi watsi da batun takarar Jerry Gana

"Ko da wani abu makamancin wannan ya taba faruwa na san an sanar da shugaban kasa kuma za a fada masa ko su waye suka yi hakan lokacin da yake zaman jinya a kasar Ingila.

"Shi da kansa shugaba Buhari ya fadi cewar akwai mutanen da suka so ya mutu, har ma sun fara neman kujerar mataimakin shugaban kasa kamar yadda shi ma Osinbajo ya tabbatar," a kalaman Farfesa Ango.

Farfesa Ango ya ce dukkan abinda ake yadawa duk jita-jita ce maras tushe balle makama.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel