Zaben 2019: PDP na son jefa rayukan ma'aikatanmu cikin hatsari - INEC

Zaben 2019: PDP na son jefa rayukan ma'aikatanmu cikin hatsari - INEC

- Rahotanni na bayyana cewa hukumar zabe ta kasa INEC na ci gaba da fuskantar zarge zage da suka, kan cewar tana kulla makircin yin magudi a zaben 2019

- PDP ta ce yunkurin hukumar INEC na kirkiro da wasu rumfunan zabe a sansanonin gudun hijira 'IDP's' a Arewacin kasar, hada bakine da APC don shirya magun zabe

- Sai dai INEC ta bayyana wannan zargi a matsayin kalaman batanci da ka kiya jefa rayukan ma'aikatan hukumar cikin hatsari a lokacin zaben

A yayin da kowacce jam'iyyar siyasa a kasar ta daura damar yakin zabe don fuskantar zabukan 2019 da ke gabatowa, hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC na ci gaba da fuskantar zarge zage da suka, kan cewar tana kulla makircin yin magudi a zaben.

A ranar Asabar, jam'iyyar PDP ta ce yunkurin hukumar INEC na kirkiro da wasu rumfunan zabe a sansanonin gudun hijira 'IDP's' a Arewacin kasar, wata hanya ce ta shirya yin magun zabe don baiwa APC damar sake komawa shugabancin kasar.

Sai dai ba tare da wani dogon lokaci ba, hukumar INEC ta fito ta mayar da martani kan wannan zargi na PDP, tana mai bayyana zargin a matsayin kalaman batanci da ka kiya jefa rayukan ma'aikatan hukumar cikin hatsari a lokacin zaben.

KARANTA WANNAN: Ko kadan baka cancanci sake zama shugaban Nigeria ba - PDP ta shaidawa Buhari

Zaben 2019: PDP na son jefa rayukan ma'aikatanmu cikin hatsari - INEC

Zaben 2019: PDP na son jefa rayukan ma'aikatanmu cikin hatsari - INEC
Source: Depositphotos

A bangaren martanin jam'iyya mai mulki ta APC kan wannan zargi na PDP kuwa, ta ce 'yan Nigeria sun gaji da sauraron karairayin PDP na yau da kullum, tare da kalubalantar jam'iyyar akan ta sanar da 'yan Nigeria dalilin da zai sa su sake zabarsu.

Da yake fara kyasta wutar musayar kalaman a jiya, sakataren watsa labarai na PDP na kasa, Mr Kola Ologbondiyan, a wani taron manema labarai yayi nuni da cewa gaba daya sansanonin gudun hijirar da ke a fadin kasar suna cikin yankunan da dama can akwai rumfunan zabe a ciki.

Haka zalika PDP ta yi zargin cewa fadar shugaban kasa ta umurci INEC da ta bude wasu sabbin rumfunan zabe a yankunan sahara da iyakokin kasar da Chadi da Niger, tare da kuma yin amfani da rumfunan zaben don cimma manufarsu ta farko, wato yin magudi a zaben mai zuwa.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel