Ko kadan baka cancanci sake zama shugaban Nigeria ba - PDP ta shaidawa Buhari

Ko kadan baka cancanci sake zama shugaban Nigeria ba - PDP ta shaidawa Buhari

- PDP ta ce ko kadan Buhari bai cancanci ya sake zama shugaban kasar Nigeria a karo na biyu ba, la'akari da irin rashin katabus da ya nuna a shugabancin kasar

- Jam'iyyar ta ce gwamnatin Buhari ta lalata tattalin arzikin kasar tare da jefa mafi yawan 'yan Nigeria cikin talauci da kuncin rayuwa

- Don haka jam'iyyarmu ke kira ga daukacin 'yan Nigeria da su kasance masu dakon shekara mai zuwa tare da zabar Atiku Abubakar, don sake farfado da tattalin arzikin kasar

Jam'iyyar adawa ta PDP ta ce ko kadan shugaban kasa Muhammadu Buhari bai cancanci ya sake zama shugaban kasar Nigeria a karo na biyu ba, la'akari da irin rashin katabus da ya nuna a shugabancin kasar na tsawon shekaru uku da rabi da ya kwashe akan mulkin.

Jam'iyyar a cikin wata sanarwa daga sakataren watsa labaranta na kasa, Kola Ologbondiyan ta ce gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta yi almubazzaranci da lalata tattalin arzikin kasar tare da jefa mafi yawan 'yan Nigeria cikin talauci da kuncin rayuwa, tana mai jaddada cewa ya zama wajibi a tsige Buhari a zabe mai zuwa.

KARANTA WANNAN: Dalilin da yasa na rufe ofishin yakin zaben Buhari a Oyo - Dr Adebayo Shittu

"Bayan yin dogon nazari kan jawabkin shugaban kasa Muhammadu Buhari na cewar akwai matsatsin rayuwa da kasar zata sake fuskanta a shekaru masu zuwa, jam'iyyar PDP ta bayyana wannan kalami a matsayin abun razanarwa, wanda karara ke nuna cewa Buhari na son kuntatawa 'yan Nigeria.

Ko kadan baka cancanci sake zama shugaban Nigeria ba - PDP ta shaidawa Buhari

Ko kadan baka cancanci sake zama shugaban Nigeria ba - PDP ta shaidawa Buhari
Source: Depositphotos

"Abun da cin rai ace bayan irin wahalar da 'yan Nigeria suka sha a cikin shekaru uku da rabi, iya abunda shugaban kasa Buhari zai iya yiwa 'yan Nigeria alkawari, shine wata wahalar, maki makon neman hanyoyin da zai bunkasa rayuwar al'umma.

"A kan wannan dalilin, a lokacin da shuwagabanni a fadin duniya ke gabatar da jawabai na kara kwarin guiwa ga al'ummarsu, a hannu daya shi shugaban kasarmu na yiwa al'ummarsa alkawarin tsananin rayuwa da wata ukubar a nan gaba.

"Don haka jam'iyyarmu ke kira ga daukacin 'yan Nigeria da su kasance masu dakon shekara mai zuwa cikin tsammanki da samun kyakkyawar makoma, a hannu daya kuma su kasance masu nuna goyon bayansu ga dan takararmu na shugaban kasa, Atiku Abubakar, don sake samun damar farfado da tattalin arzikin kasar da kuma bunkasa rayuwar jama'a," a cewar PDP

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel