Dalilin da yasa na rufe ofishin yakin zaben Buhari a Oyo - Dr Adebayo Shittu

Dalilin da yasa na rufe ofishin yakin zaben Buhari a Oyo - Dr Adebayo Shittu

- Dr Adebayo Shittu ya bayyana cewa wasu tarin matsaloline suka tilasta shi rufe ofishin yakin zaben shugaban kasa Muhammadu Buhari da ke karkashin kulawarsa a jihar Oyo

- A cewar Shittu, sun kasa biyan Naira miliyan uku a matsayin kudin hayar tsohon ofishin yakin zaben shugaban kasar, sai dai suna kan neman wani ofishin mai saukin kudi

- Haka zalika Shittu ya ce batu kan wai ya juyawa Buhari baya karyar ce tsagoranta kasancewar shine mukarrabin shugaban kasar na farko da ya fara yi masa yakin zabe

Dr Adebayo Shittu wanda ya kasance ministan sadarwa, ya bayyana cewa wasu tarin matsaloline suka tilasta shi rufe ofishin yakin zaben shugaban kasa Muhammadu Buhari da ke karkashin kulawarsa a jihar Oyo.

Dr Shittu wanda ya bayyana hakan a matsayin martani ga labaran da ake yadawa na cewar ya janye jikinsa a yiwa Buhari/Osinbanjo yakin zabe a jihar, ya ce batu kan wai ya juyawa Buhari baya karyar ce tsagoranta kasancewar shine mukarrabin shugaban kasar na farko da ya fara yi masa yakin zabe.

Ya ce har yanzuyana cikin gwamnatin Buhari kuma masu fada aji a cikink jkam'iyyar APC, hasalima yana daya cikin wadanda suka kafa majar jam'iyyar tare da kulla kyakkyawar alaka da shugaban kasa Buhari.

KARANTA WANNAN: Burinmu shine Buhari ya samu kuri'u 2m a jihar Oyo - Shittu

Dalilin da yasa na rufe ofishin yakin zaben Buhari a Oyo - Dr Adebayo Shittu

Dalilin da yasa na rufe ofishin yakin zaben Buhari a Oyo - Dr Adebayo Shittu
Source: Depositphotos

Dr Shittu ya bayyana cewa sun karbi hayar ofishin yakin zaben Buharin akan Naira miliyan uku kowacce shekara, sai dai daga baya biyan kudin hayar ofishin ya gagara, a hannu daya kuma mai wajen ya rinka kunno masu wuta kan lallai sai sun biya shi kudi ko su kwashe kayansu su kara gaba.

"Muna kan neman wani sabon ofishin da zai ishe mu gudanar da harkokin yakin zaben shugaban kasar wanda kudin kula da shi ba zai kai wancan na baya ba. Don haka ba gaskiya bane wai cewar bama tare da Buhari ko na janye jikina akan yi masa kamfe.

"Lokacin da suka fara yada wannan labarin basu tuntube ni ba. Wannan kuwa alama ce ta cewar awai wata manufa da ake son cimmawa akaina, kuma ba zasu samu nasara ba, domin kuwa ina tare da Buhari 100 bisa 100."

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel