Dalilin da yasa muke son Lawan ya zama shugaban majalisar dattijai - Tinubu

Dalilin da yasa muke son Lawan ya zama shugaban majalisar dattijai - Tinubu

- Asiwaju Bola Tinubu, ya bayyana dalilin da yasa shuwagabannin jam'iyyar APC ke son Ibrahim Lawan ya zama shugaban majalisar dattijai

- Ya bayyana cewa sanata Lawan ya zama abun koyi ga sauran takwarorinsa wajen kwarewa da sanin makamar shugabanci da kasar ke bukata

- Da yake jinjinawa Gwamna AJimobi na canja makomar jihar a cikin shekaru 7 da suka gabata, Tinubu ya ce kuma gamsu da zabar Adebayo Adelabu a matsayin magajin jihar

A ranar Ahamis, jagoran jam'iyyar APC na kasa, Asiwaju Bola Tinubu, ya bayyana dalilin da yasa shuwagabannin jam'iyyar suke son shugaban masu rinjaye na majalisar dattijai Ibrahim Lawan ya zama shugaban majalisar dattijan don maye gurbikn Bukola Saraki.

Ya bayyana cewa sanata Lawan ya zama kamar sha kallo kuma abun koyi ga sauran takwarorinsa wajen kwarewa da sanin makamar shugabanci da kasar ke bukata. Ya jaddada cewa bata garin 'yan siyasar kasar ne suka dakile Lawan daga nuna bajintarsa a fagen kawo ci gabawa kasar.

Tinubu wanda aka bashi damar gabatar da jawabin maraba a wani taron tattaunawa na Abiola Ajimobi da aka gudanar a Ibadan, kya jinjinawa shugaban masu rinjaye na majalisar dattijan na tsayawa tsayin daka akan aikinsa dukda irin kalubalen da ke faruwa a majalisar dama kasar baki daya.

KARANTA WANNAN: Farashin kayan abinci a Nigeria ya tashi da kashi 13.28 a watan Nuwamba - NBS

Dalilin da yasa muke son Lawan ya zama shugaban majalisar dattijai - Tinubu

Dalilin da yasa muke son Lawan ya zama shugaban majalisar dattijai - Tinubu
Source: Depositphotos

A wajen taron tattaunawar mai taken: "Hanyoyin samar da nagartattun kudurori da zasu dore wajen samar da ci gaba", tsohon gwamnan jihar Legas ya ce: "Sanata Lawan, mun gode kwarai. Nasara zata samu a gareka a majakisar. Kai babban misaline da za a rika bugawa wajen kwarewar shugabanci a kasar."

Da yake jinjinawa Gwamna AJimobi na canja makomar jihar a cikin shekaru 7 da suka gabata, Tinubu ya ce wannan nasarar tasa zata kasance kamar a banza ma damar ba a samu magaji kwararre kamarsa ba.

Ya kuma jinjinawa gwamnan na zabar Adebayo Adelabu, a matsayin wanda zai gajeshi a shugabancin jihar, yana mai bayyana zabikn a matsayin hanyar ci gaban jihar baki daya.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel