Makaryatan 'Yan Jarida sun ruwaito daga kasar Mali na fito - El-Rufa'i

Makaryatan 'Yan Jarida sun ruwaito daga kasar Mali na fito - El-Rufa'i

A yayin da shaci fadi, kalaman batanci da kuma nuna kiyayya suka zamto babbar barazana a fadin duniya wajen haddasa tarzoma, rikici gami da tashin tashina, gwamnan jihar Kaduna Mallam Nasir El-Rufa'i ya yi karin haske akan hakan.

Gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufa'i, ya nemi gwamnatin tarayyar Najeriya, akan jingina doka ga gwamnatocin jihohi da za su rika hukunta ma su yada rahotanni na shaci fadi da kuma kalaman batanci da nuna kiyayya.

El-Rufa'i ya yi wannan kira ne yayin ganawarsa da Ministan watsa labarai da al'adu na kasa, Alhaji Lai Muhammad, cikin wani bigire na daban da taron kasa karo na 47 da aka gudanar kan yakar rahotanni na shaci fadi da kalaman nuna kiyayya karo domin tabbatar da zaman lafiya da hadin kan kasa.

Gwamnan yake cewa, a halin yanzu dokar kasa ta jingina nauyin hukunta masu yada rahotanni na karya da kalaman nuna kiyayya kadai akan babbar Kotun tarayya da ya kamata jihohin kasar nan su samu makamanciyar wannan dama.

Makaryatan 'Yan Jarida sun ruwaito daga kasar Mali na fito - El-Rufa'i

Makaryatan 'Yan Jarida sun ruwaito daga kasar Mali na fito - El-Rufa'i
Source: Depositphotos

A yayin hikaito wani lamari na shaci fadi da ya faru a kansa, gwamna El-Rufa'i ya bayar da shaidar cewa, akwai wani sa'ili da ma'adana ta rahotanni na yanar gizo watau shafin wikipedia, ya wallafa cewa, El-Rufa'i ya kasance haifaffen birnin Bamako na kasar Mali.

Da yake ci gaba da hikaito barazanar rahotanni na karya da kuma kalamai na nuna kiyayya, gwamnan ya bayyana cewa, ba bu abinda ya haifar da tashin-tashinar da ta auku a yankin Kasuwar Magani da ke birnin jihar sa a kwana-kwanan nan face kalaman batanci da kuma nuna kiyayya.

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, Mallam El-Rufa'i ya yi kira da babbar murya akan hukunta dukkanin masu yada rahotanni na shaci fadi da kuma kalamai na nuna kiyayya da a cewar sa wannan lamari ya zamto tamkar karfen kafa wajen jefa kasar nan cikin rudani.

KARANTA KUMA: Majalisar tarayyar Kasar Ireland ta bai wa Mata lasisin zubar da ciki

A nasa jawaban, Ministan ya bayyana cewa, a halin yanzu zantuka na shaci fadi da kage shine babban makami da jam'iyyun adawa suka rika domin tunkarar babban zaben kasa na 2019.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, a yayin lokaci na shagulgulan bikin Kirsimeti ya gabato, farashin kayan masarufi ya fadi kasa wanwar a jihar Kaduna.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel