Sheikh Shuaibu ya nemi Buhari da Atiku su daina caccakar juna

Sheikh Shuaibu ya nemi Buhari da Atiku su daina caccakar juna

- Sheikh Abubakar Shaibu yayi kira na musamman ga Atiku da kuma Buhari

- Babban Malamin yace abin kunya ne ‘Yan takarar su rika kai wa juna hari

- Malamin ya nemi manyan ‘Yan takaran da su rika jan hankalin mabiyan su

Sheikh Shuaibu ya nemi Buhari da Atiku su daina caccakar juna

Sheikh Abubakar Shuaibu ya ja hankalin Buhari da Atiku a kan zabe mai zuwa
Source: UGC

Mun ji labari cewa wani Bajimin Malamin addini da ke birnin tarayya Abuja watau Sheikh Abubakar Sadeeq Shaibu, yayi kira na musamman ga Alhaji Atiku Abubukar da kuma Shugaban Kasa Muhammadu Buhari game da zaben 2019.

Shehin Malamin na Musulunci ya gargadi manyan takarar shugaban kasar na zaben da za ayi a shekara mai zuwa da su daina fitowa su na cin mutunci juna saboda neman mukami a daidai wannan lokaci da ake tsakiyar yakin neman zabe a kasar.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya koma kujerar sa ya gama a 2019 – Gwamna Lalong

Kamar yadda Jaridar Daily Trust ta rahoto, wannan Malami yayi wannan kira ne a wajen wanu taron Mauludin Annabi Muhammad (SAW) da aka shirya a Garin Abuja a Ranar Asabar. Malamin yace da kunya a ga ‘Yan siyasa su na fada tsakanin su.

Yayin da ake cigaba da yakin neman zaben 2019, Malamin ya nemi manyan ‘Yan takarar Shugaban kasar su ja-kunnen Hadiman su da Mukarraban su. Shehin yace a mafi yawan lokuta, Mabiyan ‘Yan siyasar ne ke tada rigima don haka a gargade su.

Wannan Malami dai ya tunawa masu neman mulki cewa Ubangiji Allah ne kurum ke daukar shugabanci ya damka sa a hannun wanda ya ga dama don haka babu dalilin a rika rigima da juna saboda siyasa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel