Ali Ndume ya roki ‘Yan Majalisa su bada hadin-kai a gabatar da kasafin kudin badi

Ali Ndume ya roki ‘Yan Majalisa su bada hadin-kai a gabatar da kasafin kudin badi

- Sanatan Borno ta Kudu Ali Ndume yayi magana kan kasafin kudin 2019

- ‘Dan Majalisar ya nemi Takwarorin sa su marawa Shugaban kasa baya

- Sanatan na APC ya kuma yi tir da kalaman Ministan kasafi na Najeriya

Ali Ndume ya roki ‘Yan Majalisa su bada hadin-kai a gabatar da kasafin kudin badi

Sanata Mohammed Ali Ndume yayi tir da kalaman Ministan kasafin kudi
Source: Depositphotos

Sanatan da ke wakiltar Mazabar Borno ta Kudu a Majalisar Dattawa, Mohammed Ali Ndume yayi kira ga ‘Yan uwan sa da ke Majalisa su ba Shugaban kasa Buhari hadin-kai domin ya gabatar da kasafin kudin Najeriya na shekarar 2019.

Sanata Ali Ndume yayi tir da kalaman Ministan kasafi na Kasar Udoma Udoma. Ndume yace idan har ta tabbata Ministan ya zargi Majalisa da kokarin kawowa Shugaba Buhari cikas a gabatar da kasafin kudin badi, lallai bai kyauta ba.

A zantawar da babban Sanatan na APC yayi da ‘Yan Jarida a Birnin Tarayya Abuja a Ranar Lahadi, ya bayyana cewa Ministan kasafin kasar ne ya jawo duk wani bacin lokaci na gabatar da kasafin kasar a gaban Majalisa ba kowa ba.

KU KARANTA: 2019: Buhari ya koma kujerar sa ya gama – Inji Gwamnan Filato

Ana rade-adin cewa wasu ‘Yan Majalisar Wakilai sun yi barazanar yi wa Shugaban kasa bore a lokacin da yake shirin gabatar da kundin kasafin kudin Kasar a gaban su. Ali Ndume yayi kira da ‘Yan Majalisar Wakilan su janye wannan shiri.

Sanatan na Borno ya ba Shugaban Kasa Buhari shawara ya gabatar da kasafin na 2019 kafin Majalisa ta tafi hutun kirismeti. ‘Dan Majalisar yace yin hakan ne zai bada dama a soma aiki kan kundin kasafin da zarar an dawo hutun shekara.

Sanata Ndume dai yana sa rai kwanan nan Majalisar Dattawa da Wakilai ta tarbi Shugaban kasar domin ya kawo masu kasafin kudin badi. Mu na da labari cewa Gwamnatin Najeriya ta shirya kashe Naira Tiriliyan 8.6 a cikin shekarar 2019.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel