Yanzu ne lokacin da zamu kawo karshen ta'addancin kungiyar Boko Haram - Buhari

Yanzu ne lokacin da zamu kawo karshen ta'addancin kungiyar Boko Haram - Buhari

A yau ne shugabannin kasashen gefen tekun Chadi suka yi wani taro a Abuja domin cigaba da tattauna yadda za a kawo karshen aiyukan ta'addanci na kungiyar Boko Haram.

Yayin ganawar ta su ta yau ne shugaba Buhari ya bayyana cewar yanzu ne lokacin da shugabannin kasashen zasu kawo karshen aiyukan ta'addanci na kungiyar Boko Haram.

Shugabannin kasashen da suka halarci taron sun hada da shugaban kasar Chadi, Idris Deby Itno; na kasar Nijar, Mahamadou Issoufou; da kuma Firaministan kasar Kamaru, Philemon Yang, wanda ya wakilci shugaban kasar Kamaru, Paul Biya.

Yanzu ne lokacin da zamu kawo karshen ta'addancin kungiyar Boko Haram - Buhari

Buhari da shgabannin kasashen gefen tekun Chadi
Source: Facebook

Taron na yau cigaba ne a kan taron da shugabannin suka yi a garin N'djamena na kasar Chadi a watan Nuwamba.

DUBA WANNAN: 2019: Shugabannin jam'iyyar SDP 37 sun yi watsi da batun takarar Jerry Gana

Da yake jawabi yayin bude taron, shugaban kungiyar kasashen gefen tekun Chadi, shugaba Buhari ya bayyana cewar yin amfani da rahoton da kwamitin ya amince da shi a zamansu na farko zai kawo canji a yaki da aiyukan ta'addanci na Boko Haram.

Da yake magana a kan yaki da kungiyar Boko Haram, shugaba Buhari ya kafe kan cewar yanzu ne lokacin da za a kawo karshen aiyukan ta'addanci na kungiyar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel