2019: Shugabannin jam'iyyar SDP 37 sun yi watsi da batun takarar Jerry Gana

2019: Shugabannin jam'iyyar SDP 37 sun yi watsi da batun takarar Jerry Gana

Shugabannin jam'iyyar SDP a jihohin Najeriya 37 sun yi watsi da hukuncin Jastis Hussein Baba Yusuf da ya kwace takarar shugaban kasa daga hannun tsohon gwamnan jihar Kuros Riba, Donald Duke, tare da mika ta ga Farfesa Jerry Gana.

A ranar Juma'a ne wata babbar kotun Abuja ta bayyana cewar Jerry Gana ne ya lashe zaben fidda 'yan takarar kujerar shugaban kasa da jam'iyyar SDP tayi a ranar 6 ga watan Oktoba, a saboda haka shine halastaccen dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar SDP.

Kotun ta ce jam'iyyar SDP ta saba ka'idar daidaito a bayyana Duke a matsayin dan takarar ta kasancewar shi da shugaban jam'iyyar, Olu Falae, sun fito ne daga yanki guda.

2019: Shugabannin jam'iyyar SDP 37 sun yi watsi da batun takarar Jerry Gana

Jerry Gana da Donald Duke
Source: Depositphotos

Duke ne ya samu nasara a zaben fidda 'yan takarar na ranar 6 ga watan Oktoba da adadin kuri'u 812, yayin da Farfesa Gana ya zo na biyu da adadin kuri'u 611. Sai dai Farfesan ya garzaya kotu tare da neman ta bayyana shi a matsayin mutumin da ya samu nasara a zaben bisa uzurin cewar Duke da Falae sun fito ne daga yanki guda, lamarin da ya saba da kundin tsarin mulkin jam'iyyar su ta SDP.

DUBA WANNAN: Shehu Sani ya fadi abinda Buhari ya yi da babu shugaba a duniya da ya taba yi

Sai dai a wani jawabi da shugabannin jam'iyyun 37 suka sa hannu a kai sun ce har yanzu Duke ne dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar a zaben shekarar 2019.

Wakilan shugabannin, Oke Idawene (shugaba) da Abubakar Dogara (sakatare) sun ce babu adalci a hukuncin kotun, kuma ba zasu taba amincewa da shi ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel