2019: APC ta yi kuskure da ta gabatar da Buhari karo na biyu - Hezekiah

2019: APC ta yi kuskure da ta gabatar da Buhari karo na biyu - Hezekiah

- Wani malamin addini yace jam’iyyar APC za ta yi danasanin sake zabar Buhari a matsayin dan takarar shugabancin kasar karo na biyu

- Farfesa Daddy Hezekiah, yace duba ga mulkin jam’iyya APC, kamata yayi ace ta gabatar da wani a madadin dan takarar shugaban kasa a zabe 2019

- Malamin yace shugaban kasar ya ba al’umman kasar kunya, cewa Buhari bai yi abubuwa don inganta tattalin arziki kasar ba

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulk za ta yi danasanin sake zabar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a matsayin dan takarar shugabancin kasar karo na biyu, inji wani malamin addini.

Farfesa Daddy Hezekiah, shugaban jam’ar Hezekiah, Umudi a jihar Imo ya bayyana cewa, duba ga mulkin jam’iyya mai mulki, kamata yayi ace APC ta gabatar da wani a madadin dan takarar shugaban kasa a zabe 2019.

Malamin wanda ya kasance sugaban cocin Living Christ Mission Church, yayi Magana da manema labarai a Owerri a ranar Asabar, 15 ga watan Disamba kan halin da kasar ke ciki.

2019: APC ta yi kuskure da ta gabatar da Buhari karo na biyu - Hezekiah

2019: APC ta yi kuskure da ta gabatar da Buhari karo na biyu - Hezekiah
Source: Depositphotos

A cewarsa shugaban kasar ya ba al’umman kasar kunya, inda ya kara da cewa Buhari bai yi abubuwa don inganta tattalin arziki da ababen mor rayuwa a kasar ba.

KU KARANTA KUMA: Shehu Sani ya fadi abinda Buhari ya yi da babu shugaba a duniya da ya taba yi

A halin da ake ciki, darakta janar na kungiyar kamfen din Atiku, Otunba Gbenga Danil yace shugaba Buhari ya gaza cika alkawarinsa na samar wa yan Najeriya ayyuka.

Tsohon gwamnan na jihar Ogun ya bayyana hakan ne a wani fitowa da yayi a shahararren shirin nan na siyasa a Channels TV.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel