Bangarori biyu da muka mayar da hankali a kai - Minisatan Buhari

Bangarori biyu da muka mayar da hankali a kai - Minisatan Buhari

- Gwamnatin tarayya ta ce za ta mayar da hankali ne wajen samar da tsaro da ayyukan yi ga 'yan Najeriya

- Wannan sakon ya fito ne daga bakin Ministan harkokin cikin gida, Laftanat Janar Abdulrahman Dambazau

- Dambazau ya yi wannan jawabin ne a wajen bikin yaye jami'an NIS karo na 43 a makarantar bayar da horo da ke Kano

Gwamnatin tarayya za ta mayar da hankali ne wajen karfafa hukumomin tsaro da kuma magance matsalar rashin ayyukan yi da ke addabar al'ummar Najeriya.

Ministan harkokin cikin gida, Laftanant Janar Abdurrahman Dambazau ne ya bayar da wannan sanarwar a wajen bikin yaye dabbin jami'an hukumar kula da shige da fice (Immigration) karo na 43 a ranar Asabar a makarantar bayar da horo na hukumar da ke Kano.

Bangarori biyu da muka mayar da hankali a kai - Minisatan Buhari

Bangarori biyu da muka mayar da hankali a kai - Minisatan Buhari
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: Sojoji sun ragargaji 'yan ta'addar Zamfara, hotunan wadanda suka mutu

Mataimakin shugaban hukumar ta Immigration Ado Ja'afar mai murabus ne ya wakilci Dambazau a wajen taron.

Ya ce yaye jami'ai 652 daga makarantar bayar da horon na Kano abu ne da ke nuni karara cewa gwamnati ta mayar da hankali wajen samar da tsaro da kuma samar da ayyukan yi da dimbin matasan da ke Najeriya.

Dambazau ya ce hukumar ta NIS za ta cigaba da himma wajen bayar da horo da tarbiyya da jami'anta domin tabbatar da cewa sun gudanar da ayyukansu kamar yadda ya dace.

Ya ce ma'aikatarsa ba za ta amince da wani rashin da'a ba daga kowanne jami'i da ke karkashin hukumomin da ke ma'aikatan wanda suka hada da NSCDC, Hukumar kula da gidajen fursuna (Prison Service), Fire Service da Immigration.

A jawabinsa, Kwantrola Janar na NIS, Muhammad Babandede ya yi kira da jami'an da aka yaye su kasance masu da'a da kuma biyaya ga dokokin aikinsu.

Babandede ya ce jami'an karo na 43 sune karo na farko ake yaye da digiri.

"Muna alfahari da wannan sabon tsarin bayar da horo na NIS domin yana daya daga cikin mafi inganci a cikin makarantun bayar da horo da ke Najeriya," inji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel