Hatsarin mota ya hallaka masallata biyu a masallacin Juma'a

Hatsarin mota ya hallaka masallata biyu a masallacin Juma'a

Wata mota kirar fijo J5 ta hallaka mutane biyu a wani masallaci a jihar Filato bayan ta kwace daga hannun direban dake tuka ta.

Motar ta kutsa cikin masallacin ne a jiya yayin da al'ummar musulmi ke halartar sallar juma'a a babban masallacin garin Yelwan Shandam, a karamar hukumar Shendam.

Shaidun gani da ido sun ce lamarin ya faru ne yayin da jama'a suka idar da sallar juma'a.

Abdullahi Salihu, limamin masallacin, ya shaidawa majiyar mu ta wayar tarho cewar motar ta yiwa wasu mata biyu muggan raunuka.

Hatsarin mota ya hallaka masallata biyu a masallacin Juma'a

Hatsarin mota ya hallaka masallata biyu a masallacin Juma'a
Source: Original

DUBA WANNAN: Sojoji sun ragargaji 'yan ta'addar Zamfara, hotunan wadanda suka mutu

"Tabbas, lamarin ya faru. Tuni yara biyu sun mutu yayin da wasu mata biyu suka samu manyan raunuka, kuma an garzaya da su asibiti domin duba lafiyar su.

"Ina can cikin masallaci lokacin da abinda ya faru amma daga baya na fito da kaina naga abinda ya faru da idona. Mun yi kokari mun kwantar da hankalin matasan da suka fusata zasu kona motar. Direban motar motar ma bamu bari sun taba shi ba, yana nan lafiya," a kalaman limamin.

Limamin ya ce mata biyun da suka sune; Khadija Dayyabu da Muhammad Kabiru.

Ya kara da cewa za a yi jana'izar su ba tare da bata lokaci ba bisa tsarin addinin Islama.

Motar dake makare da itace ta kwace wa direbanta ne bayan birkinta ya samu matsala.

Tyopev Terna, kakakin rundunar 'yan sanda a jihar Filato, bai samu damar amsa sako da kiran da manema labarai suka yi masa ba domin jin ta bakin hukumar ta 'yan sanda.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel