Muhawarar shugabannin kasa: Na kosa inyi arangama da Buhari - Atiku

Muhawarar shugabannin kasa: Na kosa inyi arangama da Buhari - Atiku

Dan takaran kjeran shugaban kasan karkashin jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa bayan kallon muhawarar mataimakinsa Peter Obi, ya kosa yayi arangama da shugaba Muhammadu Buhari.

Alhaji Atiku ya bayyana jin dadinsa ga yadda abokin tafiyansa, yayi namijin kokari a muhawarar da yayi da mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, a Abuja.

Yace: "Ina matukar alfahari da Peter Obi kan yadda ya bayyana yadda ya shimfida manufarmu na gyara Najeriya.... Na kosa ayi na yan takaran shugabannin kasa."

Peter Obi ya kara da yan takaran kujeran mataimakin shugaban kasa daga jam'iyyu biyar a daren Juma'a, 14 ga watan Disamba, 2018.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya shiga ganawar gaggawa da shugaban kasan Chadi, Nijar, da Kamaru kan Boko Haram

Rahotannin sun nuna cewa da yiwuwan shugaba Buhari ba zai halarci muhawarar da za'ayi ranan 19 ga Junairun 2019 ba saboda wasu dalilai da ba'a bayyana ba. Amma masu sharhi kan al'amuran yau da kullum sun ce ba dole bane Buhari ya halarta.

Mun kawo muku rahoton cewa Atiku Abubakar yace shugaban kasa Muhammadu Buhari da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ba za su cika alkawarin da suka daukarma kudu maso gabas na samar da shugaban kasa a 2023 idan suka marawa Buhari baya a shekara mai zuwa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel