Amurka ta bayyana zaben shekarar 2019 da 'zakaran gwajin dafi' na Afrika

Amurka ta bayyana zaben shekarar 2019 da 'zakaran gwajin dafi' na Afrika

Kasar Amurka ta ce babban zaben shekarar 2019 na Najeriya a matsayin "zakaran gwajin dafi" ga kasar da ma nahiyar Afirka.

Tibor Nagy Jr., mataimakin sakataren cibiyar harkokin Afirka ne ya fadi hakan a jawabin da ya yiwa kwamitin majalisar Amurka ta harkokin Afirka a kan inganta lafiya, kare hakokin 'yan adam da hukumomin kasa da kasa a ranar Juma'a.

"Amurka da amince da cewa babban zaben Najeriya da za a gudanar a watan Fabrairun 2019 babban jarabawa ce ga kasae," a cewar Nagy.

Tawagar da Amurka ta ce zaben shekarar 2015 babban nasara ce da demokradiyar Najeriya duk da cewa akwai wasu 'yan matsaloli da aka samu yayin gudanar da zaben.

DUBA WANNAN: Sojoji sun ragargaji 'yan ta'addar Zamfara, hotunan wadanda suka mutu

Zaben Najeriya ta 2019 babban jarabawa ce ga Afirka - Amurka

Zaben Najeriya ta 2019 babban jarabawa ce ga Afirka - Amurka
Source: Facebook

"Gabanin zaben na 2019, Amurka za ta cigaba da bawa Najeriya goyon bayan da ta ke bukata domin gudanar da sahihiyar zabe a cikin zaman lafiya wadda 'yan Najeriya za suyi na'am da shi,"

"Ta hanyar diplomasiyya da wayar da kan mutane wanda suka hada da matasa da kungiyoyin sa kai da shirye-shiryen karfafa demokradiya da gudanar da mulki, muna taimakawa kasar karfafa demokradiyar ta da hukumomin ta.

"Amurka ba ta da wani dan takara da ta ke goyon baya. Muna goyon bayan demokradiya ce wadda za ta haifar da zabe cikin zaman lafiya da al'ummar Najeriya za su amince da shi." inji shi.

Ya ce Amurka ta tsara wani shiri da zai mayar da hankali a kan abubuwa uku, abubuwan kuma sune bayar da gudun mawa don ganin an gudanar da sahihiyar zabe, taimakawa hukumomin Najeriya da makamashin aiki da kuma sanya idanu a kan zaben.

Na uku kuma shine kare afkuwar rikici bayan zabe ta hanyar wayar da kan al'umma a kan muhimmancin zaman lafiya da sulhu tsakanin mutane.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel