A karon farko Janar IBB ya dawo bayan shugaba Buhari kan batun tsaro, yayi masa jinjina

A karon farko Janar IBB ya dawo bayan shugaba Buhari kan batun tsaro, yayi masa jinjina

- IBB ya bayyana Buhari a matsayin wanda yayi nasara akan rashawa

- Ya bayyana hakan ne a sakon taya shi murnar zagayowar ranar haihuwar sa daya aike masa

- Buhari dai zai cika shekaru 76 a duniya a ranar Litinin 17 ga watan Disamba

A karon farko Janar IBB ya dawo bayan shugaba Buhari kan batun tsaro, yayi masa jinjina

A karon farko Janar IBB ya dawo bayan shugaba Buhari kan batun tsaro, yayi masa jinjina
Source: Facebook

Tsohon shugaban soja Ganar Ibrahim Badamasi Babangida IBB ya bayyana shugaban kasa Muhammad Buhari a matsayin wanda yayi nasara akan rashawa da rashin tsaro da ake fama dashi a kasar.

IBB ya bayyana hakan ne a wani sakon taya murnar zagayowar ranar haihuwar sa daya aike masa a ranar Asabar.

Shugaban kasa Muhammad Buhari zai cika shekara 76 a duniya a ranar Litinin 17 ga watan Disamba 2018.

DUBA WANNAN: Wasu iyali na kuka kan wai 'yansandan NAjeriya na kare wanda ya kashe musu yaro

IBB ya bayyana cewa "Shugaban kasa Muhammad Buhari ya zama abin koyi ga yan siyasa manya da yara,saboda hanyoyin daya bi wajen tseratar da kasar mu daga halin da take ciki".

"Ka samu nasara mai yawa akan kawar da rashawa,ta'addanci, rashin tsaro da kuma fitar da kasar daga kangin tattalin arziki ".

"Abin farin ciki ne a shekarar ka ta 76 duba da kalubalen dake cikin shugabanci amma kayi amfani da karfin ka dan ganin ka kawo cigaba a kasar".

A siyasance dai, an sha raba gari tsakanin manyan Janar-Janar na kasar nan da shugaba Buhari, inda IBB yake jigo a PDP, shi kuma Buhari yake APC.

Babu dai ko lokaci daya da Buhari ya kai ziyara Minna a fili bayan hawansa mulki, duk da an taba ganin IBB din a taron kasa a Villa sau daya a 2015.

Babangidan ne dai ya hambaras da gwamnatin Buhari/Idiagbon a 1985, ya kuma kulle shi shekaru, ya sako wadanda Buharin ya kulle, lamari da ya hada su gabar shekaru.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa.

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel