Sojin Najeriya sun dagawa UNICEF kafa, bayan zargin leken asiri da ake musu a baya

Sojin Najeriya sun dagawa UNICEF kafa, bayan zargin leken asiri da ake musu a baya

- Sojin Najeriya sun janye kudurin su na janye aiyukan yaran cibiyar Unicef

- Sojin sunce hakan ya biyo bayan tattaunawa da jami'an Unicef

- Akwai bukatar wakilan Unicef su dinga sanar da jami'an da yakamata kafin su dauka ko horar da sababbin ma'aikata

majalisar

majalisar
Source: Depositphotos

Sojin Najeriya sun janye takunkumin su da suka kakabawa aiyukan UN na karkashin cibiyar Unicef a arewa maso gabas na kasar nan kan harkar agazawa 'yan gudun hijira da yara da yaki da Boko Haramun ya tagayyara.

Sojin sun ce hakan ya biyo bayan tattaunawar da sukayi da jami'an Unicef ta gaggawa.

A ranar juma'a, Sojin sun zargi cibiyar da yi wa 'yan ta'addan addinin Islama na Boko Haram leken asiri a yankin.

Miliyoyin mutane a yankin arewa maso gabas din da ta'addancin y'an Boko Haram yasa suka bar yankin sun dogara ne da taimakon mutane ha irin wadannan hukumomi.

A wata maganar kuma, Sojin sunce, sun dage soke aiyuka ma'aikatan Unicef din na wata uku a yankin.

A baya ma, sojin su dakatar da aikin UNICEFF din bayan ma'aikatanta sun bada rahoton wai soji na lalata da 'yan mata a sansanonin gudun hijirar, kafin su basu agaji. Sojin sun karyata hakan, amma an san halin soji da mata a filayen yaki a duniya.

DUBA WANNAN: Labarin yadda ma'aikacin banki ya tafka 419 ta miliyoyin Nairori

Sun ce a yayin taron, "mun hori wakilan Unicef dasu tabbatar da sun sanar da hukumomin da suka dace kafin su dauka ko fara horar da sababbin ma'aikata."

Maganar tazo ne sa'o'i kadan bayan da sojin suka zargi cibiyar UN da yi wa 'yan ta'addan leken asiri.

"Ma'aikatan Unicef ne ke horarwa tare da tura 'yan leken asiri wadanda ke taimakon yan ta'addan," inji Sojin a baya, bayan sun sami rashin fahimtar juna.

Sojin suka kara da cewa, irin wannan lamurra na fahimtar juna, zasu cigaba da taimaka musu da kuma durkushe fada da ta'addanci," inji Sojin.

Wannan ba shine karo na farko da sojin suka dau mataki akan cibiyar ba.

Yankin arewa maso gabas na Najeriya ya dade yana fuskantar mummunan ta'addancin Boko Haram.

Sama da mutane dubu 30,000 suka rasa rayukan su kuma wasu suka rasa muhallin su a kokarin mayakan da sai sun tabbatar da shari'ar Islama a yankin.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa.

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel