Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya shiga ganawar gaggawa da shugaban kasan Chadi, Nijar, da Kamaru kan Boko Haram

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya shiga ganawar gaggawa da shugaban kasan Chadi, Nijar, da Kamaru kan Boko Haram

An kaddamar wata ganawa mai muhimmanci tsakanin shugabanni kasashen yankin tafkin Chadi yanzu a cikin birnin tarayyar Najeriya, Abuja kan karashe magana akan yadda za'a kawo karshen rikicin Boko Haram.

Ana wannan ganawar ne bayan irinta da aka gudanar a watan Nuwamba a babbar birnin Chadi, N'djamena wanda shugaba Buhari ya jagoranta yayinda yan kungiyar tada kayar bayan Boko Haram suka kai mumunan hari barikin sojin dake Matele, arewacin jihar Borno.

Shugabannin kasashen da suke halarce sune Shugaba Muhammadu Buhari, shugaba Mahamadou Issoufou na Nijar, Firam minista Philemon Yang wanda ya wakilci shugaban kasan, Paul Biya, Shugaba Deby na Chadi.

KU KARANTA: FAYYACE GASKIYA: A muhawarar jiya, yadda Peter Obi na PDP ya zuba karerayi

A jawabin bude taron, shugaba Buhari wanda shine jagoran kungiyar kasashen yankin Chadi ya ce tabbatar wannan takarda da kwamitin zatayi zai taimaka matuka wajen yaki da boko Haram

Shugaba Buhari ya bayyana musu cewa wannan yaki ne wanda sai an gama shi. Sauran wadanda suke halarce sune manyan hafsoshin hukumar sojin Najeriya.

Jaridar Daily Trust ta bada rahoton cewa shugabannin sun shiga ganawar sirri wanda ake kyautata zaton za'a kwashe sa'o'i biyar anayi.

A karshen wannan ganawa, za'a bayyanawa jama'a wannan sabon usulubi da za'ayi amfani dashi wajen yakin Boko Haram.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel