Wasu iyali na kuka kan wai 'yansandan NAjeriya na kare wanda ya kashe musu yaro

Wasu iyali na kuka kan wai 'yansandan NAjeriya na kare wanda ya kashe musu yaro

- Yan sanda suna kare wanda ya kashe mana dan mu cewar wasu iyalai

- An nemi su biya kudi N35,000 dan a basu form din bincike

- Wani jami'in dan sanda ne ya kashe shi

Wasu iyali na kuka kan wai 'yansandan NAjeriya na kare wanda ya kashe musu yaro

Wasu iyali na kuka kan wai 'yansandan NAjeriya na kare wanda ya kashe musu yaro
Source: Depositphotos

Iyalan Tariela Nikade wanda yake dalibi a jami'ar Niger Delta( NDU) inda yake shekara ta Uku,ana zargin jami'in dan sanda Timadi Emmanuele ya kashe shi a ranar 23 ga watan Nuwamba 2018 a Yenagoa.

Babban yayan wanda aka kashe din ya bayyana cewa a kokarin su na ganin anbi musu hakkin su akan kashe dan uwanshi da akayi an nemi su biya kudi N35,000 dan a basu form din bincike.

Abin mamaki wai yan sanda suna neman iyalan yaron su biya N35,000 dan a basu form din bincike.

DUBA WANNAN: Jam'iyyar APGA na magagin wargajewa gabanin 2019

A wani hannun kuma iyalan suna tuhumar yan sandan da kin maida hankali wajen gudanar da bincike bare su mikawa kotu jami'in daya kashe musu dan uwa,amma sunzo suna bukatar kudi daga garesu.

A bangaren hukumar yan sandan sunce suna cigaba da bincike akan lamarin sannan nan bada dadewa ba zasu mika wanda ake zargin kotu.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa.

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel