Tattalin arzikin Najeriya na cikin mawuyacin hali - Buhari

Tattalin arzikin Najeriya na cikin mawuyacin hali - Buhari

A jiya, Juma'a, ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gargadi gwamnoni da ragowar shugabanni a kan su kara kulla damara domin fuskantar tsananin da ya fi na baya saboda halin da tattalin arzikin kasa ke ciki.

Shugaba Buhari ya yi wannan kalami ne yayin ganawar sa ta sirri da gwamnonin kasar nan jiya a Abuja.

Gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari, ne ya bayyana hakan ga manema labarai bayan kammala ganawar su da shugaba Buhari.

A cewar gwamnan, shugaba Buhari ya sanar da su cewar tattalin arzikin Najeriya na cikin mawuyacin hali, tare da kalubalantar su a kan bullo da hanyoyin da za a inganta tattalin arzikin.

Tattalin arzikin Najeriya na cikin mawuyacin hali - Buhari

Buhari da gwamnonin
Source: Depositphotos

A cewar Yari, "Shugaban kasa, kamar koda yaushe, ya shaida mana halin da tattalin arzikin kasa ke ciki tare yi mana tuni a kan bukatar mu hada kai domin yin tunani a kan hanyoyin magance matsalar tattalin arziki a kasar nan.

"Maganganun da ya yi mana sun fi yawa ne a kan bukatar mu kara kulla damara domin ganin mun dora tattalin arzikin Najeriya a kan hanyar da ta dace.

DUBA WANNAN: Manyan 'yan siyasa 6 da gwamnatin Buhari ta daure

"Dukkaninmu shugabannin ne, har wadanda ba zasu koma kujerar gwamna ba, a saboda haka zamu yi aiki tare domin ceto tattalin arzikin Najeriya.

"Al'amura zasu kara tsanani, kamar yadda shugaban kasar ya sanar da mu."

Taron na shugaba Buhari da gwamnonin na jiya ya tattauna ne a kan hanyoyin da za a habaka hanyoyin shigowar kudi domin samun sukunin yin aiyukan da zasu kawo cigaban kasa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel