FAYYACE GASKIYA: A muhawarar jiya, yadda Peter Obi na PDP ya zuba karerayi

FAYYACE GASKIYA: A muhawarar jiya, yadda Peter Obi na PDP ya zuba karerayi

Domin fayyace gaskiya ga al'ummar Najeriya da kuma nuna yadda yan siyasa ke karerayi domin hayewa mulki, mun tattaro muku irin karerayin da akayi a muhawarar masu takaran kujeran mataimakin shugaban kasa da akayi jiya.

Jam'iyyun siyasan da sukayi musharaka sune; Allied Congress Party of Nigeria (ACPN), Alliance for New Nigeria (ANN), All Progressives Congress (APC), Peoples Democratic Party (PDP) da Young Progressives Party (YPP).

Kalli jerin maganganun da dan takaran PDP, Peter Obi, ya zuba karerayi ga yan Najeriya:

1. IKIRARIN OBI: Akwai motoci miliyan biyu a Najeriya

GASKIYAR MAGANA: Game da rahoton hukumar lissafin Najeriya, akwai kimanin motoci 11,547,236 a Najeriya a lissafin karshen da akayi

2. IKIRARIN OBI: Najeriya ta fadi warwas a lissafin kai da kai na duniya daga matsayin 124 zuwa 127

GASKIYAR MAGANA: Karya ne. Game da cewar gamayyar tattalin arzikin duniya. Najeriya ta kara matsayi daga 124 zuwa 114.

3. IKIRARIN OBI: A shekarar 2015, masu sanya hannun jari daga kasashen wajen sun kashe $21bn a 2015, amma a 2017 ya sauko $12bn.

GASKIYAR MAGANA: Karya ne. Game da rahoton hukumar lissafin Najeriya, a shekarar 2015 $9.6bn ne, a 2017 $12.3 bn ne.

4. IKIRARIN OBI: Kasuwanci tsakanin kasashen Afrika a yau ya dawo kasa da kashi 1 cikin 10

GASKIYAR MAGANA: Karya ne. Game da cewar bankin shiga da ficen Afrika, Afrexim, kasuwanci tsakanin kasashen Afrika kimanin kashi 15 cikin 100 ne.

5. IKIRARIN OBI: Mai zai baku kudin canji sama da kashi 80 cikin 100

GASKIYAR MAGANA: Game da cewar NBS a 2017, kudin da Najeriya ta samu na canji sama da kashi 90 cikin 100 ne.

6. IKIRARIN OBI: Kamfanin Apple ta fi kasar Najeriya, South Afrika da Misra tattalin arziki

GASKIYAR MAGANA: Karya ne. Arzikin Apple a yau $788.57 billion ne.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel