Majalisar tarayyar Kasar Ireland ta bai wa Mata lasisin zubar da ciki

Majalisar tarayyar Kasar Ireland ta bai wa Mata lasisin zubar da ciki

A yayin da Hausawa kan ce na zaune bai ga gari ba, hakan take kuwa yayin da dokokin kasashen duniya suka bambanta da na wasu kasashen. Hakan ya kan jefa mamaki a zukatan al'ummar wasu kasashen da zarar sun samu rahoton wata doka da ta sabawa ta kasar su.

Kamar yadda shafin jaridar BBC Hausa ya ruwaito, kuduri na dokar da ke fafutikar halasta zubar da ciki a kasar Ireland da ke nahiyyar Turai ya shallake dukkan matakai a zauren majalisar dokoki ta kasar.

A yammacin ranar Alhamis din da ta gabata, rahoto a kasar Ireland ya bayyana cewa, kudirin halasta dokar zubar da ciki ga Mata masu juna biyu ya kai mataki na karshe na bayar da lasisi da sahalewar dokokin kasar Ireland.

Majalisar tarayyar Kasar Ireland ta bai wa Mata lasisin zubar da ciki

Majalisar tarayyar Kasar Ireland ta bai wa Mata lasisin zubar da ciki
Source: Getty Images

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, wannan doka kiris ya rage ta tabbata yayin da za a mika ta gaban shugaban kasar Ireland, Michael D. Higgins, domin ya rattaba hannu.

Tarihi da binciken manema labarai ya tabbatar da cewa, kasar Ireland ta yi watsi da wannan doka ta lasisin zubar da ciki a watan Mayun da ya gabata biyo bayan kuri'ar raba-gardama da 'yan kasar suka kada.

KARANTA KUMA: Ku daina raki, ku jajirce bisa aiki tukuru - Osinbajo ga Gwamnonin Najeriya

Simon Harris, Ministan lafiya na kasar Ireland, ya bayar da shaidar wannan rahoto a shafinsa na zauren sada zumunta inda ya bayyana goyon bayan sa akan hakan.

Sai dai ko shakka ba bu wannan kudiri na doka ya bayar da dama ta zubar da cikin da bai wuce makonni 12 ba, a yayin da kwararrun lafiya suka tabbatar da rashin lafiyar dan tayin da ke ciki ko kuma mai dauke da junan biyu na fuskantar barazana ta rasa rayuwarta.

Kazalika jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, yawaitar amfani da tabarau ba bisa ka'ida ba na barazana da gurbata lafiyar idanu.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel