Zaben 2019: Amurka ta ce rikici ya tunkaro Najeriya

Zaben 2019: Amurka ta ce rikici ya tunkaro Najeriya

Dangane da gabatowar babban zaben kasa na 2019, al'amari na ci gaba da gudana a kasar nan yayin da kasashen duniya suka zuba idanu domin ganin yadda za ta kaya a fadin Najeriya. A yayin da wasu ke kyautata zato wasu na sabanin haka.

A halin yanzu dai, gwamnatin kasar Amurka, ta bayyana fargabarta kan babban zaben kasa na Najeriya da za a gudanar a badi, in da ta ke hasashen ba bu wani abu da zai mamaye shi face rikici gami da tashin-tashina.

Gwamnatin Amurka ta bayyana cewa, gudanar zaben ka iya haifar da munanan tasirai bisa ga tafarkin dimokuradiyyar Najeriya, yankin Afirka ta Yamma da kuma nahiyyar baki daya.

Sai dai gwamnatin Amurka kamar yadda majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito ta yi hasashen cewa, ba bu lallai rikita-rikitar da zaben zai haifar ta kasance mai girma a fadin kasar, illa iyaka a wasu 'yan tsirarun yankunan ta.

Tibor Nagy

Tibor Nagy
Source: UGC

Mataimakin babban sakataren gwamnatin Amurka kan harkokin kasashen nahiyyar Afirka, Tibor Nagy, shine ya bayyana hakan yayin gabatar da jawabansa kan zaben Najeriya na 2019 a zauren majalisar wakilai ta kasar da ke birnin Washington a jiya Alhamis.

Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Abubakar Bukola Saraki, tare da wasu 'yan majalisar tarayyar Najeriya sun halarci zaman majalisar da ya gudana a babban birnin na kasar Amurka.

Mista Nagy ya jaranton yankunan Najeriya da ka iya fuskantar wannan tashin-tashina yayin zaben 2019 da suka hadar jihar Kano, Ribas, Benuwe, Filato, da kuma jihar Borno.

KARANTA KUMA: Dole Buhari ya sha kasa a zaben 2019 - Jerry Gana

A yayin da yake barrantar da kasar Amurka daga goyon bayan kowane dan takara a Najeriya, Mista Nagy ya bayyana cewa, kasar ta na goyon bayan ingataccen zabe na gaskiya da ya tsarkaki daga kowane nau'i na magudi.

Ya kuma jaddada cewa, kasar Amurka za ta bayar tallafi ga Najeriya daidai gwargwadon iko wajen tabbatar da kwararar romon dimokuradiyya maras yankewa. Ya kuma yi kira ga hukumomin tsaro na kasar nan kan sanya idanun lura ga wadanda ka iya haddasa tarzoma yayin zaben na badi.

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, a ramar Alhamis din da gabata, shugaban majalisar dattawa na Najeriya tare da tawagarsa ta wasu 'yan Majalisar tarayya, sun halarci bikin kaddamar da tsare-tsaren ci gaban nahiyyar Afirka da shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya assasa.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel