2019: Shugaba Buhari shine mafi kyawun zabi a Najeriya - APC reshen Amurka

2019: Shugaba Buhari shine mafi kyawun zabi a Najeriya - APC reshen Amurka

A yayin da babban zaben kasa na 2019 ke ci gaba da danno da kai, ko shakka ba bu jam'iyyu da dama na ci gaba da kai komo na goyon bayan wakilan su domin cimma nasara ta lashe kujerun siyasa daban-daban a fadin kasar nan.

Jam'iyyar APC reshen birnin Houston na kasar Amurka, ta nemi daukacin al'ummar Najeriya kan goyon bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari, a yayin babban zaben kasa na 2019.

Reshen jam'iyyar ya yi wannan kira ne inda ta nemi goyon bayan al'ummar kasar nan wajen bai wa shugaban kasa Buhari dama ta kammala kyawawan aikace-aikace gami da managartan kudiri na fidda kasar nan zuwa ga tudun tsira.

Majiyar Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, jam'iyyar APC reshen kasar Amurka na ci gaba da wannan kira domin bai wa shugaba Buhari dama ta kammala dashen magarcin tubali domin inganta rayuwar al'umma da kuma bunkasar tattalin arzikin kasa.

2019: Shugaba Buhari shine mafi kyawun zabi a Najeriya - APC reshen Amurka

2019: Shugaba Buhari shine mafi kyawun zabi a Najeriya - APC reshen Amurka
Source: Depositphotos

Jam'iyyar reshen kasar Amurka ta yi wannan kira ne tare da hadin gwiwar al'ummar yankin Afirka ta Yamma da ke cirani a birnin Abuja, inda suka nemi Matasa da su fito kwansu da kwarkwata wajen kada kuri'un su ga shugaban kasa Buhari.

Kazalika jam'iyyar na hasashen shugaba Buhari zai dasa tubalai managarta ga Matasa da za su jingina da dodanar gajiyar sa mai riba a shekarar 2023.

Shugaban jam'iyyar shiyyar Amurka, Elder Chime, shine ya yi wannan kira da cewa, zaben shugaban kasa na 2019 zai gudana ne tsakanin shugaba Buhar da kuma tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar.

Mista Chime ya misalta shugaba Buhari da Atiku a matsayin jiga-jigan 'yan takara da ke wakilta manyan jam'iyyun kasar nan watau APC da kuma PDP. Ya ke cewa, zaben zai gudana ne tsakanin na gari da Mugu, saboda haka dole Matasa su mike tsaye wajen tabbatar da jakadancin na gari.

KARANTA KUMA:

Jam'iyyar yayin zayyana kyawawan akidu gami da nagarta da kuma nasarorin gwamnatin shugaba Buhari a bisa karagar sa ta mulki, ta ce ba bu wani dan takara mafi dace gami da cancanta da kuma kyawu ta fuskar jagorancin kasar nan face shugaban kasa Buhari.

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, cibiyar bayar da kariya da mutunta 'yan jarida, ta bayyana cewa akwai adadin 'yan jarida 251 da ke garkame a gidajen kaso da ke fadin kasashen Duniya a halin yanzu.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel