Cikin Hotuna: Muhawarar 'yan takara 5 manema kujerar mataimakin shugaban kasa a Zaben 2019

Cikin Hotuna: Muhawarar 'yan takara 5 manema kujerar mataimakin shugaban kasa a Zaben 2019

A daren jiya na Juma'a, 'yan takara biyar ma su hankoron kujerar mataimakin shugaban kasa a zaben 2019 sun tafka muhawara a tsakanin su da juna domin baja kolin dalilai ga al'ummar kasar nan na kada masu kuri'u a zaben na badi.

Cibiyar tafka muhawara kan zabe ta Najeriya, NEDG, Nigerian Election Debate Group, tare da hadin gwiwar kungiyar watsa labarai ta kasa, BON, Broadcasting Organisation of Nigeria, su ke da alhakin daukar nauyin wannan babban taro da aka gudanar a Otel din Transcorp Hilton da ke garin Abuja.

Cikin Hotuna: Muhawarar 'yan takara 5 manema kujerar mataimakin shugaban kasa a Zaben 2019

Cikin Hotuna: Muhawarar 'yan takara 5 manema kujerar mataimakin shugaban kasa a Zaben 2019
Source: UGC

Eddi Emisiri, babban sakataren kungiyar NEDG, ya zayyana cewa, jam'iyyun biyar da suka fuskanci juna yayin wannan muhawara sun hadar da ACPN (Allied Congress Party of Nigeria), ANN (Alliance for New Nigeria), APC (All Progressives Congress), YPP (Young Progressives Party) da kuma jam'iyyar PDP (Peoples Democratic Party).

Wakilan jam'iyyun biyar da suka fafata da juna yayin muhawarar sun hadar da:

1. Yemi Osinbajo (APC)

2. Peter Obi (PDP)

3. Umma Getso (YPP)

4. Alhaji Abdulganiyu Galadima (ACPN)

5. Khadijah Abdullahi-Iya (ANN)

KARANTA KUMA: Manyan 'yan siyasa 6 da gwamnatin Buhari ta daure

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, muhawara a tsakanin 'yan takarar biyar ta gudana kan al'amurran da suka shafi kasar nan kama daga tattalin arziki, ta'addanci gami da rashin tsaro, ilimi, harkokin lafiya da kuma mu'amalar Najeriya da kasashen ketare.

Kazalika jaridar ta ruwaito cewa, dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar SDP, Farfesa Jerry Gana, ya bayyana cewa kayar da shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben 2019 ya zama wajibi kuma tilas.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel