Donald Duke ya yi magana a kan kwace takarar sa da kotu tayi

Donald Duke ya yi magana a kan kwace takarar sa da kotu tayi

Dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar Social Democratic Party, (SDP), Donald Duke, ya ce zai daukaka kara a kan hukuncin da kotu ya yanke a yau na kwace masa tikitin takarar shugabancin kasa na jam'iyyar.

Babban kotun tarayya da ke zamanta a Maitama Abuje ne a yau Juma'a ta ce tsohon Ministan Sadarwa na Najeriya, Jerry Gana ne dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar ta SDP.

Mr Duke ya lashe takarar ne bayan da jam'iyyar ta gudanar da zaben fidda gwani a watan Oktoban 2018 inda ya samu kuri'u mafi rinjaye a kan Mr Gana.

Sai dai Mr Gana ya shigar da kara a kotu inda ya kallubalanci sakamakon zaben bisa tsarin karba-karba na jam'iyyar da ta ce shugaban jam'iyya da dan takarar shugabancin kasa ba za su kasance daga yanki guda ba.

Donald Duke ya yi magana a kan kwace takarar sa da kotu tayi

Donald Duke ya yi magana a kan kwace takarar sa da kotu tayi
Source: Facebook

A hukuncin da ya zartas, mai shari'a Hussein Baba-Yusuf ya ce dole ne dukkan mambobin jam'iyyar suyi biyaya ga dokokin da ke cikin kundin tsarin jam'iyyar.

DUBA WANNAN: Sojoji sun ragargaji 'yan ta'addar Zamfara, hotunan wadanda suka mutu

Ya ce tsarin karba-karba da ke cikin kundin tsarin jam'iyyar ya ce ba zai yiwa shiugaban jam'iyya da dan takarar shugabancin kasa su fito daga yanki guda ba.

"A yanzu, shugaban jam'iyyar, Cif Olu Falae ya fito daga Kudu ne kuma shima Duke daga Kudu ya fito. Doka ta yi bayani karara, babu wani abin jayaya a nan.

"Doka ya ce jam'iyyun siyasa suyi biyaya da dokokin da suka kafa da kansu. "Mai shigar da kara ya gabatar da hujoji da suka gamsar da kotu, an saba kundin tsarin mulkin jam'iyyar, kotu ba za ta iya goyon bayan saba doka ba," inji shi.

Alkalin ya soke zaben da akayi a baya, ya kuma bukaci SDP ta mika sunan Gana ga hukumar INEC a matsayin dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar a zaben 2019. Bugu da kari, ya umurci Duke ya dena gabatar da kansa a matsayin dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar

Mr Duke ya shaidawa manema labarai a Legas cewa: "Duk da cewa muna jiran cikaken bayani daga kotu, muna sake jadada cewa mu masu biyaya ne ga doka da kundin tsarin mulki."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel