Dole Buhari ya sha kasa a zaben 2019 - Jerry Gana

Dole Buhari ya sha kasa a zaben 2019 - Jerry Gana

Mun samu cewa, dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Farfesa Jerry Gana, ya yi wani furuci mai sanya faduwar gaba ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, dangane da yadda za ta kaya a babban zaben kasa na badi.

Dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar SDP, Farfesa Jerry Gana, ya bayyana cewa ya zama wajibi kuma tilas ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sha kasa a yayin babban zabe na 2019.

Dole Buhari ya sha kasa a zaben 2019 - Jerry Gana

Dole Buhari ya sha kasa a zaben 2019 - Jerry Gana
Source: Depositphotos

Farfesa Gana ya bayyana hakan ne a yau Juma'a cikin garin Abuja, jim kadan bayan da babbar kotun tarayya ta tabbatar da shi a matsayin dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyyar SPD.

Tsohon Ministan sadarwar na Najeriya ya bayyana cewa, kasancewar sa dan takara a halin yanzu, ya zama wajibi shugaban kasa Buhari ya sha babban kayi da tun a yanzu ya kamata ya fara tattara komatsan sa daga fadar Villa domin kuwa an kayyade kwanakin da suka rage masa.

KARANTA KUMA: Buhari ya kalubalanci gwamnoni kan inganta ci gaban gine-gine

Ya kuma yi tarayya da sauran jam'iyyun adawa dangane da kiran shugaba Buhari akan amincewa da gyara dokar zaben kasar nan, inda ya ce hakan zai tabbatar da gudanar ingataccen zabe na gaskiya da ya tsarkaka daga duk wani nau'i na magudi.

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko, mai wakilcin shiyyar Sakkwato ta Arewa, ya bayyana cewa babban burin sa a halin yanzu shine, Matasa su kauracewa bangar siyasa kuma su jefa kuri'un su ga shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben 2019.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel