Da duminsa: Magoya bayan dan takarar shugaban kasa sun mamaye harabar wurin muhawara

Da duminsa: Magoya bayan dan takarar shugaban kasa sun mamaye harabar wurin muhawara

- Magoya bayan dan takarar shugabancin kasa na African Action Congress, Omoyele Sowore sun mamaye harabar wurin muhawar

- Sun bukaci lallai da bawa jam'iyyarsu dama shiga cikin muhawarar kamar yadda aka baiwa sauran jam'iyyu

- Sun dau alwashin cewa ba za su dena zanga-zangar ba har sai an fito fili an fadawa duniya dalilin da yasa aka ware jam'iyyarsu daga muhuwarar

Da duminsa: Magoya bayan dan takarar shugaban kasa sun mamaye harabar wurin muhawara

Da duminsa: Magoya bayan dan takarar shugaban kasa sun mamaye harabar wurin muhawara
Source: Twitter

Kimanin magoya bayan dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar African Action Congress, Omoyele Sowore 50 ne suka gudanar da zanga-zanga a dakin taro na Transcorp Hilton da ke Abuja domin nuna rashin jin dadinsu kan ware shi daga jerin 'yan takarar da za su gwabza a muhawara da za ayi gabanin zaben 2019.

DUBA WANNAN: Sojoji sun ragargaji 'yan ta'addar Zamfara, hotunan wadanda suka mutu

Masu zanga-zangar suna hallara dakin taron dauke da alluna masu sakonni daban-daban da ke cewa gwagwarmayar da su keyi na neman ganin anyi adalci ne kuma ba za su taba karaya ba.

A cewarsu, za su cigaba da yin zanga-zangar saboda ba a bayyana dalilin da yasa aka ware dan takarar shugaban kasar na AAC ba daga muhawarar.

Mai magana da yawun masu zanga-zangar, Jude Eya ya shaidawa manema labarai cewa bai dace a ware Sowore da mataimakinsa daga cikin muhawarar ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel