2019: Wamakko ya bukaci 'yan Nigeria da su zabi Buhari tare da kaucewa shiga rikicin siyasa

2019: Wamakko ya bukaci 'yan Nigeria da su zabi Buhari tare da kaucewa shiga rikicin siyasa

- Sanata Aliyu Magatakardar Wamakko ya bukaci matasan Nigeria da su zabi shugaban kasa Muhammadu Buhari a babban zaben 2019

- Ya ce gwamnatin Buhaari ta baiwa matasa muhimmanci, yana mai cewa lokaci yayi da suma matasan za su sakawa gwamnatin ta hanyar sake zabarta a 2019

- Ya kara da cewa sa hannun shugaban kasa kan dokar nan ta "Ban yi karanta da tsayawa takara ba" alama ce ta cewar shugaban kasa Buhari ya damu matuka da matasa

Sanata Aliyu Magatakardar Wamakko ya bukaci matasan Nigeria da su zabi shugaban kasa Muhammadu Buhari a babban zaben 2019, kana ya kuma bukace su da su kauracewa dukkanin wani nau'i na ta'addanci.

Wamakko ya yi wannan kiran a ranar Alhamis a cikin wata sanarwa da ya turawa kamfanin jarida na Daily Trust, ta hannun mai bashi shawara kan kafofin watsa labarai, Farfesa Dagaci Aliyu Manbe.

Ya ce gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhaari mai ci a yanzu ta baiwa matasa muhimmanci, musamman ta wajen bunkasa rayuwarsu, yana mai cewa lokaci yayi da suma matasan za su sakawa gwamnatin ta hanyar sake zabarta a 2019.

KARANTA WANNAN: Ra'ayin Jerry Gana kan hukuncin kotu na bashi takarar shugaban kasa a jam'iyyar SDP

2019: Wamakko ya bukaci 'yan Nigeria da su zabi Buhari tare da kaucewa shiga rikicin siyasa

2019: Wamakko ya bukaci 'yan Nigeria da su zabi Buhari tare da kaucewa shiga rikicin siyasa
Source: Depositphotos

"Shirin bunkasa rayuwar matasa na N-Power wanda gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta bullo, an samar da shi ne domin bunkasa rayuwar matasa kai tsaye, don haka ya kamata suma matasan su sakawa gwamnatin da mafifin alkairi.

"Don haka ina kira ga 'yan Nigeria, musamman matasa da su fito kwansu da kwarkwatarsu don zabar shugaban kasa Muhammadu Buhari a babban zaben 2019 mai zuwa," a cewar sanarwar.

Ya kara da cewa sa hannun shugaban kasa kan dokar nan ta "Ban yi karanta da tsayawa takara ba" alama ce ta cewar shugaban kasa Buhari ya damu matuka da matasa kuma ya gina harsashe na basu damar cimma muradunsu na siyasa.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel