Ra'ayin Jerry Gana kan hukuncin kotu na bashi takarar shugaban kasa a jam'iyyar SDP

Ra'ayin Jerry Gana kan hukuncin kotu na bashi takarar shugaban kasa a jam'iyyar SDP

- Farfesa Jerry Gana, ya jinjinawa hukuncin da babbar kotun Abuja ta yanke na tabbatar da shi a matsayin halastaccen dan takarar jam'iyyar SDP

- Tsohon ministan ya kara bayyana cewa tuni ya rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiyar da kwamitin zaman lafiya na kasa karkashin Janar Abdulsalami Abubakar ya gabatar

- A ranar Juma'a kotun ta yanke wannan hukunci, inda ta yi watsi da tsohon gwamnan jihar Cross River Donald Duke a matsayin dan takarar jam'iyyar

Tsohon ministan watsa labarai da harkokin masarautu, kuma dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar Social Democratc Party SDP, Farfesa Jerry Gana, ya jinjinawa hukuncin da babbar kotun Abuja ta yanke na tabbatar da shi a matsayin halastaccen dan takarar jam'iyyar.

Da ya ke zantawa da manema labarai a Abuja, Farfesa Gana ya ce wannan hjukuncin da kotun ta yanke wata babbar nasara ce ta demokaradiyya da kuma siyasar jam'iyya, duba da cewar cusa akidar dan takara da jam'iyya ke yi ya daina tasiri a siyasar kasar.

Tsohon ministan ya kara bayyana cewa tuni ya rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiyar da kwamitin zaman lafiya na kasa karkashin Janar Abdulsalami Abubakar ya gabatar da kuma shiryawa taron tafka muhawara kan hakan na zaben 2019.

KARANTA WANNAN: Ko anki ko anso: Tattalin arzikin Nigeria na cikin mawuyacin hali - Buhari

Ra'ayin Jerry Gana kan hukuncin kotu na bashi takarar shugaban kasa a jam'iyyar SDP

Ra'ayin Jerry Gana kan hukuncin kotu na bashi takarar shugaban kasa a jam'iyyar SDP
Source: Depositphotos

A ranar Juma'a kotun ta yanke wannan hukunci, inda ta yi watsi da tsohon gwamnan jihar Cross River Donald Duke a matsayin dan takarar jam'iyyar tare da tabbatar da Farfesa Gana a matsayin halastaccen dan takarar.

Farfesa Gana ya shigar da kara kotu inda ya bukaci da a tabbatar da shi a matsayin wanda ya lashe zaben fiytar da gwani na jam'iyyar, ta hanyar la'akari da tsarin jam'iyyar na shiyyar.

Ya shigar da kara kotun ne a lokacin da jam'iyyar SDP ta sanar da sunan Mr Duke a matsayin wanda ya lashe zaben fitar da gwanin da jam'iyyar ta gudanar a ranar 16 ga watan Oktoba.

A cewar jam'iyyar, tsohon gwamnan ya samu kuri'u 812, wanda ya bashi nasara akan tsohon ministan wanda ya samu kuri'u 611.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel