Shugaba Buhari yayi wa duniya alkawarin zabuka karbabbu

Shugaba Buhari yayi wa duniya alkawarin zabuka karbabbu

- Zaben 2019 na Najeriya na ta matsowa

- Dan takarar shugabancin kasa karkashin jam'iyyar PDP Atiku Abubakar ya fara yakin neman zabe

- An zabi Najeriya a matsayin cibiyar talauci ta duniya

Shugaba Buhari yayi wa duniya alkawarin zabuka karbabbu

Shugaba Buhari yayi wa duniya alkawarin zabuka karbabbu
Source: Twitter

Zaben 2019 na ta matsowa, Atiku Abubakar ne ya zamo dan takarar shugabancin kasa karkashin jam'iyyar PDP inda shugaban kasa Muhammadu Buhari ne na jam'iyyar APC.

Abubakar, tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya ya fara yakin neman zaben shi akan Buhari ta hanyar bayyana abubuwan dake ci ma yan Najeriya tuwo a kwarya kamar su hauhawar rashin aikin yi da talauci, tare da cigaban rashin tsaro a tsakiyar kasar ta Najeriya.

Kwanan nan ne Brookings Institution ta zabi Najeriya a matsayin babbar cibiyar talauci ta duniya.

Rikon rashin kular kuwa da akewa tattalin arzikin kasar ne ya zamo babbar matsalar kasar.

A 2016, kasar ta shiga halin kaka ni kayi ta fannin tattalin arzikin ta na farko a shekaru 25 sakamakon faduwar farashin man fetur da kuma hare haren yankin Naija Delta, yankin da ake samun mai na kasar. Duk da fitar kasar daga halin a 2017, cigaban kasar na tafiyar hawainiya sannan kayayyaki na ta tashi a farashin su.

DUBA WANNAN: Sabon garambawul da za'a yiwa matatun man kasar nan bayan tazarce

Masu zuba hannayen jari suka fara karanci a kasar.

An fara shirye shiryen zaben kenan tsakanin mazaje biyun sai kwatsam Obiageli Ezekwesili, mace mai kamar maza dake da kakkarfan tarihin shugabancin tattalin arziki ta bayyana don takarar shugabancin kasar karkashin jam'iyyar ACPN. Yanayin yakin neman zaben ta shine na dawo wa da yan Najeriya burikan su.

Ezekwesili mai shekaru 55 na kokarin ganar da matasa cigaban fasaha wadanda suma kalubale ne a kasar da abokan adawar ta, Buhari mai shekaru 75 da Atiku mai shekaru 71 basu gane ba.

Duka da kokarin ganar da matasan da take yi, su sunfi son matashi irin su wanda zai fahimci bukatar su tare da magana da yawun su a kasar da fiye da kashi 50 na mutanen ta suna da shekaru kasa da 30 ne.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa.

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel